Izala Ta Yi Matsaya kan Zaben 2027 a Taron da Gwamnoni Suka Halarta a Jos
- Kungiyar JIBWIS ta bayyana cikakken goyon bayanta ga matsayar Shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, kan zaben 2027
- JIBWIS ta kuma yi kira ga Musulmi da sauran ’yan Najeriya da su shiga harkokin siyasa cikin lumana, gaskiya, adalci da kishin ƙasa
- Ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar ƙarshen taro da ta fitar bayan kammala taron ƙasa kan shiga siyasa da tabbatar da adalci a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026, a Jos
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis-Sunnah (JIBWIS), mai hedikwata a Jos, ta bayyana matsayarta kan siyasa da zaben 2027, tare da jaddada buƙatar adalci, gaskiya da shugabanci nagari a Najeriya.
Kungiyar ta bayyana haka ne a ƙarshen wani taron ƙasa da ta shirya, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026.

Source: Facebook
Ibrahim Maina Muhammad ya wallafa a Facebook cewa taron ya samu halartar sama da mutane 350 da suka haɗa da malaman addinin Musulunci, ’yan siyasa, malamai, ƙwararru, matasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Matsayar Izala kan zaben 2027
JIBWIS ta ce Musulmi, kamar sauran ’yan ƙasa, suna da haƙƙi da alhakin shiga harkokin siyasar Najeriya cikin lumana da mutunci.
Kungiyar ta jaddada cewa ya kamata shiga siyasa ya kasance bisa gaskiya, cancanta, adalci, kiyaye kundin tsarin mulki da kishin al’umma, ba tare da ƙiyayya ba.
Sai dai ta bayyana matsaya mai ƙarfi kan batun zaben 2027, musamman dangane da batun tsarin “Muslim-Muslim”.
A cewar sanarwar:
“Mun bayyana ba tare da wata shakka ba cewa mu, dukkan sahihan mambobin JIBWIS daga dukkan jihohin Najeriya, muna da cikakken goyon bayan duk wata matsaya da Shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yanke dangane da zabukan ƙasa na 2027, musamman batun Muslim-Muslim.”
Kiran shiga siyasa cikin lumana
Kungiyar ta yi kira ga Musulmi da su riƙa shiga harkokin siyasa ta hanyar yin rajistar zaɓe, jefa ƙuri’a, shiga ƙungiyoyin siyasa da kuma yin muhawara mai amfani.
Ta kuma buƙaci matasa da mata da su fahimci cewa siyasa ba kawai fafatawa ce ta neman mulki ba, hanya ce ta hidimtawa al’umma da kare muradun jama’a.
JIBWIS ta ce ya kamata ’yan siyasa su fifita muradun ƙasa a kan son kai, ƙabilanci, addini ko wata manufa ta jam’iyya.

Source: Facebook
Izala ta yi kira kan tsaro
Kungiyar ta nuna damuwa kan matsalolin tsaro da suka addabi wasu sassan Najeriya, ciki har da ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci.
Ta yaba wa Rundunar Sojin Najeriya, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayukan ’yan ƙasa.
Sai dai ta buƙaci gwamnati ta ƙara inganta tattara bayanan sirri, haɗin gwiwar hukumomin tsaro, horas da jami’ai da samar musu da kayan aiki.

Kara karanta wannan
Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
Haka kuma, JIBWIS ta yi kira da a magance tushen matsalar rashin tsaro, ciki har da talauci, rashin aikin yi, jahilci da sauran su.
Kungiyar ta kuma bukaci jami’an tsaro su ƙara ƙoƙari wajen ceto kimanin yara 78 da aka sace daga azuzuwa a garuruwan Borno.
Adalci da haɗin kan Najeriya
JIBWIS ta bayyana cewa bambancin addini, kabila da al’adu da ke akwai a Najeriya ya kamata a ɗauke shi a matsayin ƙarfi, ba abin da zai haddasa rarrabuwar kai ba.
Ta yi kira ga ’yan Najeriya da su guji ƙiyayya, ƙabilanci da nuna wariya, tare da tabbatar da adalci ga dukkan 'yan ƙasa.
Kungiyar ta ce ba za a samu haɗin kan ƙasa mai ɗorewa ba tare da adalci ba, tana mai jaddada cewa adalcu zai ƙara ƙarfafa amincewa tsakanin al’ummomin Najeriya.
Batun ’yancin faɗar albarkacin baki
Kungiyar ta ce ’yancin faɗar albarkacin baki muhimmin ɓangare ne na tsarin dimokuraɗiyya, amma ya kamata a yi amfani da shi yadda ya dace.
Ta yi kira da a rika suka mai ma’ana, muhawara da bayyana ra’ayoyi cikin lumana, tare da yin Allah-wadai da tunzura jama’a zuwa tashin hankali, yaɗa labaran ƙarya da kalaman ƙiyayya.
Haka kuma, ta buƙaci ’yan siyasa, malaman addini, ’yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta su riƙa amfani da kalamai masu kyau wajen inganta zaman lafiya.
Kira ga gwamnatoci a Najeriya
JIBWIS ta yi kira ga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da sauran ’yan Najeriya da su haɗa kai wajen gina ƙasa mai adalci, zaman lafiya da tsaro.
Kungiyar ta kuma yaba wa gwamnatin tarayya kan wasu shirye-shiryen raya ƙasa da ta ce ana aiwatarwa a fannonin abubuwan more rayuwa, ilimi, lafiya, noma, tallafa wa matasa da bunƙasa tattalin arziki.
Sai dai ta buƙaci a tabbatar da cewa ana aiwatar da waɗannan shirye-shirye cikin adalci da gaskiya a dukkan yankunan ƙasar ba tare da la’akari da ƙabila, addini ko siyasa ba.
Taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Kano, Yobe, Sokoto, Sanata Barau Jibrin da sauran manyan 'yan siyasa.
Malamai sun goyi bayan Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa sama da malamai, masu wa’azi da limamai 500 daga yankunan Arewa sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake komawa kan mulki a zabe 2027.
Goyon bayan ya biyo bayan wata ganawar sirri da suka yi da wasu gwamnonin Arewa shida na jam’iyyar APC da sauran manyan jami’an siyasa.
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Umar Namadi na Jigawa, Abba Kabir Yusuf na Kano, Mai Mala Buni na Yobe, Ahmad Aliyu na Sokoto, Uba Sani na Kaduna da Dikko Radda na Katsina.
Asali: Legit.ng



