Zance Ya Kare: NAF Ta Fitar da Cikakken Bayani kan Jirgin Saman da Ya Yi Hatsari a Najeriya
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta tabbatar da cewa jirgin da ya yi hatsari a yankin Igbokoda na Karamar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo jirginta ne
- Ta bayyana cewa jirgin kirarbATR-42 yana kan hanya ne daga Benin zuwa Legas lokacin da hatsarin ya afku da sanyin safiyar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026
- NAF ta ce ta fara aikin neman jirgin da ceto nan take tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa da jami’an agajin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta tabbatar da cewa jirgin helikwafta da ya yi hatsari a yankin Igbokoda na Karamar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo jirginta ne.
An ce jirgin, mai lamba ATR-42, yana kan wani aiki ne na yau da kullum daga Benin zuwa Legas lokacin da hatsarin ya afku da sanyin safiyar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026.

Source: Getty Images
Leadership ta rahoto cewa daraktan Hulda da Jama’a da Bayanan Rundunar Sojin Sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Wane mataki rundunar soji ta dauka?
Ejodame ya ce rundunar sojin saman Najeriya ta fara aikin neman jirgin da ceto nan take bayan hatsarin.
Ya ce ana gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa da hukumomin bayar da agajin gaggawa domin tabbatar da an yi komai yadda ya dace.
A cewarsa:
“Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta fara aikin neman jirgin da ceto nan take bayan hatsarin jirgin helikwafta ATR-42 a yankin Igbokoda na Jihar Ondo a ranar 5 ga Oktoba, 2026.”
Yadda jirgin ya rikito ya fada teku
An ce jirgin yana tafiya ne daga Benin zuwa Legas lokacin da ya yi hatsari a kusa da yankin Larada Street da ke Ilaje, inda rahotanni suka nuna cewa ya fada cikin wani kogi.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa jami’an agajin gaggawa da hukumomin tsaro sun tattara jami’ansu zuwa wurin bayan faruwar lamarin.

Source: Original
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, Jimoh Abayomi, shi ma ya tabbatar da hatsarin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ko sunayensu ba. Haka kuma, har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba.
Ana sa ran aikin neman jirgin da ceto da ake ci gaba da gudanarwa zai samar da karin bayani kan abubuwan da suka kai ga hatsarin da kuma halin da mutanen da ke cikin jirgin suke ciki.
Gwamnatin tarayya ta yi magana
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ya tabbatar da hatsarin wani jirgin sojoji dauke da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgi bakwai.
Keyamo ya ce jirgin mai lambar rajista NGR 931 ya bace ne yayin da yake kan hanyar Benin zuwa Lagos da misalin ƙarfe 9:13 na safe kafin daga bisani a samu labarin ya yi hatsari.
Asali: Legit.ng

