Gwamnonin Arewa 6 da Malaman Addini 500 Sun Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasarsu a 2027

Gwamnonin Arewa 6 da Malaman Addini 500 Sun Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasarsu a 2027

  • Malaman addini sama da 500 daga sassa daban-daban na Najeriya sun bayyana dan takarar da za su marawa baya a zaben 2027
  • Malaman sun bayyana goyon bayansu ne bayan wata ganawa da manyan ’yan siyasar APC daga Arewa a jihar Jigawa
  • Goyon bayan ya zo ne tun kafin zaben shugaban kasa na 2027, yayin da ayyukan siyasa ke kara daukar zafi a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Fiye da malaman addinin Musulunci, masu wa’azi da limamai 500 daga sassa daban-daban na Najeriya sun amince da sake zaben Shugaba Bola Tinubu a wa’adi na biyu.

Malaman addinin sun bayyana matsayar ta su ne kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu, bayan wata ganawar sirri da aka gudanar a jihar Jigawa.

Shugaba Bola Tinubu ya samu goyon baya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A wani bidiyo da kafar Nigerian affairs Journal ta sanya a shafinta na X, ta ce malaman sun gana da gwamnonin jihohin Arewa shida na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau.

Kara karanta wannan

"Ba sabon alkawari ba"; Abin da Gwamna Radda zai yi kamfen da shi a Katsina

Gwamnoni da jiga-jigai sun halarci taron

Hakazalika sun gana da Ibrahim Masari, wanda ke rike da mukamin mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan harkokin siyasa.

Taron ya hada manyan ’yan siyasar Arewa da dama tare da shugabannin addini, lamarin da ke nuna fara kokarin karfafa goyon bayan Shugaban kasar tun kafin zaben 2027. Ba a bayyana sunayen gwamnonin APC shida da suka halarci taron nan take ba.

Masari, wanda ya dade yana kawance da Tinubu a siyasa, ya taka muhimmiyar rawa wajen hulda da ’yan siyasa a madadin Shugaban kasar tun lokacin yakin neman zaben 2023, abin da ya sanya kasancewarsa a taron ta zama abin lura.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau, wanda ke wakiltar Kano ta Arewa kuma yana daga cikin manyan ’yan siyasar Arewa a Majalisar Dattawa shi ma ya halarci taron.

Malamai sun goyi bayan Tinubu

Bayan kammala ganawar, malaman addinin Musulunci da suka halarta sun bayyana a hukumance cewa suna goyon bayan Tinubu ya koma fadar Aso Rock domin yin wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

Goyon bayan da malaman sama da 500 daga sassan kasar suka bayyana na daga cikin manyan hadin kan goyon bayan da al’ummar Musulmi a Najeriya suka nuna wa Tinubu tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023.

An fara shirye-shiryen 2027

Zaben shugaban kasa na 2027 yana da sauran kusan watanni shida, amma harkokin siyasa sun riga sun fara kara daukar zafi a fadin kasar.

Da alama bangaren Tinubu na kokarin samun gagarumin goyon baya daga yankuna daban-daban da kuma kungiyoyin addini yayin da aka fara yakin neman zabe.

Malaman addini sun goyi bayan Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wajen taro Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dalilin rashin Wike a kwamitin kamfen din Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai iya zama Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027 ba.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers wanda yanzu shi ne ministan Abuja ya tabbatar da cewa hakan ba zai yiwu ba saboda ba ɗan jam'iyyar APC mai mulki ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng