Shettima Ya Dura Jihar Katsina, an Raba Miliyoyin Naira Kyauta
- Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce Najeriya za ta ba mata damar da ta dace da irin kokarin da suke yi wajen tafiyar da sana'o'insu
- Shettima ya bayyana hakan ne a Katsina yayin da ya kaddamar da rabon tallafin jari ga mata 'yan kasuwa, inda sama da mata 40,000 suka ci gajiyar shirin
- Mataimakin shugaban kasar ya kuma kaddamar da motocin bas 32 masu amfani da CNG da kekunan adaidaita sahu masu amfani da lantarki 200
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bukaci a samar da yanayin kasuwanci mai kyau ga mata a Najeriya, yana mai cewa kasar za ta taimaka masu.
Shettima ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, yayin kaddamar da rabon kudin CIF karkashin shirin NFWP-SU,

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu

Source: Facebook
Hadimin mataimakin shugaban kasa, Stanley Kingsley Nkwocha ne ya wallafa bayanan da Kashim Shettima ya yi a wajen taron a Facebook.
Mata 40,000 za su amu tallafin
Mataimakin shugaban kasar ya ce sama da mata 40,000 a jihar Katsina sun cancanci samun jarin kasuwanci bayan sun cika sharudan cancanta tare da nuna kwazo wajen ajiya da ayyukan kungiyoyinsu.
Ya ce shirin na da muhimmanci wajen taimaka wa mata su bunkasa sana'o'insu, kara samun kudin shiga da kuma inganta tattalin arzikin gidajensu.
Shettima ya ce bai kamata a dauki karamin jari a matsayin alamar karamin buri ba, domin girman sana'ar mace ba lallai ya nuna girman burinta ba, yana iya nuna irin damar samun jari da take da ita.
Ya ce mata sun dade suna daukar nauyi mai yawa da karancin kayan aiki, don haka ya kamata a samar musu da karin damar cika burinsu.
Kiran Shettima ga mata
Shettima ya bukaci matan da za su ci gajiyar shirin su ci gaba da aiki tukuru, kiyaye bayanan harkokin kasuwancinsu da kuma kula da amana tsakanin kungiyoyinsu.
Ya ce bayar da kudi kadai ba zai wadatar ba, domin ana bukatar ilimi da tsari domin kudin ya samar da sakamako mai dorewa.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci masu kula da rabon kudin da su tabbatar da cewa cancanta ce kawai tushen samun tallafin, ba tare da nuna bambanci ko tsoma siyasa ba.
Radda ya kara raba N4bn
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya ce gwamnatin jihar ta kara ware N4bn domin aiwatar da shirin.
Ya ce hakan ya kai jimillar kudin da jihar ta ware wa shirin zuwa N8bn, yana mai cewa manufar ita ce fadada damar tattalin arziki ga mata da inganta rayuwarsu.

Source: Facebook
Radda ya kuma yaba da yadda shirin ya hada mata kurame, musamman ta hanyar samar da kungiyoyin hadin gwiwa da za su ba su damar shiga shirin.
Maganar goyon bayan Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci 'yan Najeriya su kasance masu sassauci ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shettima ya bayyana hakan ne a Legas bayan ganawa da Tinubu, wanda ya dawo Najeriya bayan kammala hutunsa na shekara-shekara.
Mataimakin shugaban kasar ya kare wasu daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur da hada tsarin canjin kudin kasashen waje.
Asali: Legit.ng

