Abdulaziz Yari Ya Fadi Me za Su Yi bayan Karbar Darkatan Kamfen din Tinubu

Abdulaziz Yari Ya Fadi Me za Su Yi bayan Karbar Darkatan Kamfen din Tinubu

  • Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban Ƙasa na APC, Abdul’aziz Yari, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa jam’iyyar za ta cika alkawuran da ta ɗauka a 2023
  • Yari ya ce APC za ta ci gaba da tsayawa kan alkawuran da ta yi wa al’umma, yayin da take shirin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Ya bayyana hakan ne ranar Lahadi jim kaɗan bayan dawowarsa Najeriya, inda magoya baya da abokan siyasa suka tarbe shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC, Abdul’aziz Yari, ya yi magana kan shirin jam’iyyar na tunkarar zaben shugaban ƙasa na 2027.

Yari, wanda ke wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa APC za ta cika alkawuran da ta yi yayin kamfen ɗin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shawarci Yari game da nema wa Tinubu kuri'a a zaben 2027

Sanata Abdulaziz Yari da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu tare da Sanata Abdulaziz Yari a Villa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta rahoto cewa Sanata Yari ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a Abuja kwanaki kadan bayan nada shi jagoran yakin neman tazarcen Tinubu.

Yari: 'APC za ta cika alkawura'

Yari ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da yake magana da manema labarai bayan isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja daga wata tafiya zuwa ƙasar waje.

The Nation ta rahoto ya ce jam’iyyar APC tana da ƙudurin tabbatar da dukkan alkawuran da ta ɗauka ga ’yan Najeriya.

Ya ce:

“Ina son tabbatar wa ’yan Najeriya cewa duk wani alkawari da muka yi yayin kamfen, za mu cika shi. A yau mun ga shi [Bola Ahmed Tinubu] yana matsayin shugaban kasa, kuma da yardar Allah zai kasance shugaban kasa a 2027.”

Yari ya ce taron magoya bayan da suka tarbe shi a filin jirgin ya nuna irin amincewar da suke da ita ga shugaba Tinubu da jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Wike, NDC ta fadi yadda ta shirya kwace Abuja a 2027

Yari ya roƙi a zabi Tinubu

Yari ya nuna godiya ga magoya bayan da suka fito domin tarbarsa, yana mai cewa sun zo ne domin yi masa addu’a da kuma fatan samun nasara ga Shugaba Tinubu.

Ya kuma roƙe su da su ci gaba da bai wa shugaban ƙasa da jam’iyyar APC goyon baya yayin da ake shirin babban zaben 2027.

“Jama’ar nan sun zo ne domin su yi mini addu’a da kuma yi wa mai girma shugaban kasa fatan samun nasara.
“Jam’iyyarmu ta yi suna wajen cika alkawari. Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya ba shi hikimar jagorantar wannan ƙasa. Muna tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za mu cika dukkan alkawuranmu na kamfen,”

In ji shi.

Sanata Abdulaziz Yari a majalisa
Lokacin da Sanata Abdulaziz Yari ke magana a zauren majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

APC na shirin cin zaben 2027

Yari ya kuma bayyana fatansa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da kasancewa a kan madafun iko bayan wa’adin mulkin Tinubu na biyu.

Ya yi kira ga ’yan jam’iyyar da su haɗa kai wajen ƙarfafa matsayinta a faɗin ƙasar domin samun nasara a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tun kafin lokaci, an kammala tsara wanda zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Ya ce:

“Muna addu’ar jam’iyyarmu za ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da ke jagorantar ƙasar bayan wa’adin mulkin Shugaba Tinubu na biyu.”

Kiran Kwankwaso ga Abdulaziz Yari

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya roƙi Abdul’aziz Yari da ya sake tunanin karɓar shugabancin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027.

Kwankwaso ya yi wannan kira ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, yayin da yake mayar da martani kan tsarin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da aka kafa, wanda Tinubu zai jagoranta, yayin da Yari zai kasance Darakta Janar.

Tsohon gwamnan Kano ya tambayi dalilin da zai sa Yari, wanda ya taɓa zama gwamnan Zamfara, ya jagoranci kamfen ɗin neman ci gaba da mulkin gwamnatin da yake cewa har yanzu tana fuskantar ƙalubalen tsaro, talauci da rashin aikin yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng