Cikakken Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Kokari a Jarrabawar NECO a Shekarar 2026

Cikakken Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Kokari a Jarrabawar NECO a Shekarar 2026

  • Abia ta zama jihar da ta fi kowace jiha samun sakamako mai kyau a jarrabawar NECO a shekarar bana
  • Sakamakon NECO 2026 ya nuna babu wata jiha daga Arewa da ta shiga cikin jihohi 10 da suka fi kowa bajinta
  • Fiye da 80% na wadanda suka yi jarrabawar a shekarar nan sun yi nasara a Abia, haka abin yake ga daliban Ebonyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Jihar Abia ce ta samu mafi kyawun sakamako a jarrabawar Hukumar Shirya Jarabawar Najeriya (NECO) a bana.

A shekarar nan ta 2026, Abia ta jagoranci jerin jihohi 10 da suka fi yin kokari sosai a jarrabawar ta gama karatun sakandare.

NECO.
Wasu dalibai lokacin darasin lissafi a makaranta a Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abia da Ebonyi sun ciri tuta a NECO

Tribune ta ce sakamakon bana sun nuna cewa 81.78% na daliban da suka rubuta jarrabawar a jihar Abia sun samu nasara.

Jihar Ebonyi ce ta zo ta biyu da nasarar kashi 81.03, yayin da Ekiti ta zo ta uku inda kashi 77.68 na dalibanta suka ci jarrabawar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi yunkurin kashe ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Najeriya

Premium Times ta ce wannan ce shekara ta biyu a jere da Abia ta yi abin a yaba a jarrabawar NECO.

Delta, Osun da Legas suna biye a baya

Delta ta kasance ta huɗu da kashi 75.17 na nasara, sai Osun ta zo ta biyar da kashi 74.31 na galabar wadanda suka yi NECO.

Lagos ta zo ta shida da kashi 74.15 a jarrabawar bana. Tazararta ba ta da nisa sosai da makwabciyarta Oyo mai nasarar 74.12%.

Imo a Kudu maso gabas ta zo ta takwas, kashi 74.10 na daliban jihar sun ci jarrabawar. Bambancin da ke tsakaninta da Oyo kadan ne.

Bayelsa da Ogun ne suka cike jerin jihohi 10 na farko kamar yadda alkluma suka nuna.

73.92% na daliban da suka fito daga jihar ta Bayelsa sun yi abin kwarai a shekarar nan, haka kuma 73.34% na daliban jihar Ogun.

Cikakken jerin jihohi 10 da nasararsu a NECO

1. Abia — 81.78%

2. Ebonyi — 81.03%

3. Ekiti — 77.68%

4. Delta — 75.17%

Kara karanta wannan

'Babban abin da zai raba Bola Tinubu da mulkin Najeriya a 2027'

5. Osun — 74.31%

6. Lagos — 74.15%

7. Oyo — 74.12%

8. Imo — 74.10%

9. Bayelsa — 73.92%

10. Ogun — 73.34%

Cikin jihohin da suka yi fice a bana, babu wata daga Arewa da ta yi abin a yaba idan aka duba kason wadanda suka iya yin nasara.

Idan aka duba, za a ga cewa duka zakarun jihohin sun fito ne daga Kudu maso gabas, Kudu maso kudu da kudu maso yamma.

Sai dai wannan bai nufin wadannan jihohi sun fi kowane ilmi a kasar nan, sakamakon ya na nufin nasara ne a jarrabawar ta NECO.

Yan makaranta
Dalibai yan makaranta a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Galabar Kano a jarrabawar NECO

Ana da labari cewa idan dai a yawan wadanda suka samu nasara a akalla darassa biyar ne, jihar Kano ce ta zo ta ɗaya a NECO a bana.

Dalibai 74,413 suka samu nasarar cin 'credit' biyar ciki har da darussan Turanci da Lissafi a sakamakon bana da aka fitar a makon jiya.

Wannan ne karo na biyu a jere da Kano ke samun wannan nasara bayan ta zama ta ɗaya a shekarar 2025 a zunzurutun yawan masu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng