Halin da Ake ciki a Ondo bayan Mummunan Hatsarin Jirgin Sama da Ya Kashe Mutane
- Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce har yanzu ba a gano wani da ya tsira ba bayan wani jirgin sojan sama
- Mutane 32 ne suka kasance cikin jirgin, ciki har da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai, yayin da jami’ai ke ci gaba da bincike
- Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin mutanen da suka mutu, tare da umartar a gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Igbokoda, Ondo - Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yi magana game da mummunan hatsarin jirgin saman sojoji da ya afku a jihar.
Aiyedatiwa ya ce har yanzu ba a gano wani mutum da ya tsira ba bayan hatsarin jirgin sojan sama da ya hallaka mutane.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, sa’o’i kadan bayan jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya fadi a yankin Igbokoda, karamar hukumar Ilaje, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Mutanen gari sun fadi abin da ya faru lokacin da jirgin sojojin Najeriya ya yi hatsari
Bayanan da Gwamna Aiyedatiwa ya samu
Aiyedatiwa ya ce mazauna yankin, jami’an ceto da jami’an tsaro sun gudanar da bincike a wurin hatsarin, amma ba su gano wanda ya tsira ba.
Gwamnan ya ce ya samu bayanai daga jami’an da ke wurin cewa babu wani mutum da aka gano da rai bayan hatsarin.
Ya ce mai ba shi shawara kan harkokin tsaro ya tuntubi shugaban Amotekun da shugaban karamar hukumar Ilaje domin samun karin bayani.
Mutane 32 ne suka kasance cikin jirgin, ciki har da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai, kamar yadda aka bayyana.
Jirgin yana gudanar da wani aiki ne daga Benin City ta jihar Edo zuwa Lagos kafin ya fadi a Igbokoda.
Hatsarin ya faru ne jim kadan bayan karfe 9:00 na safe, yayin da jirgin ke kan hanyar zuwa Lagos.
Wata mazauniyar yankin mai suna Dayo Akinte, mai shekaru 39, ta ce ta ji wani sauti da ta dauka kamar aradu.

Source: Original
Aiyedatiwa ya ce babu wata alamar gobara da aka gani a wurin, don haka jami’an ruwa suka jira kafin su matsa kusa da wurin hatsarin.
Bayan tabbatar da cewa babu gobara ko fashewa, jami’an rundunar sojin ruwa suka shiga wurin domin kokarin ceto mutanen da ke cikin jirgin.
Kokarin da jami'ai ke yi a Ondo
Hukumar kula da ayyukan gaggawa ta karamar hukumar da mazauna yankin sun kuma shiga aikin neman wadanda hatsarin ya rutsa da su.
Rundunar Amotekun ta Ilaje ma ta isa wurin domin taimakawa wajen gudanar da aikin ceto, amma ba a samu wanda ya tsira ba.
Jami’an ceto sun gano tarkacen jirgin, wasu sassan fikafikan jirgin, katunan shaida da kuma wasu kayan sawa na jami’an soja.
Gwamnan ya ce rundunar sojin saman Najeriya na kokarin gano musabbabin hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutanen da ke cikin jirgin.
Tinubu ya yi alhini, ya umarci bincike

Kara karanta wannan
Jirgin rundunar sojojin Najeriya ya yi hatsari, ana fargabar mutane da dama sun mutu
An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alhini kan mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sojan, tare da umartar a gudanar da bincike.
Tinubu ya ce hatsarin lokaci ne mai matukar radadi ga rundunar sojin Najeriya da daukacin al’ummar kasar.
Ya ce jami’an sojin saman Najeriya na sadaukar da rayukansu a kullum wajen kare kasar, kuma ba za a manta da sadaukarwarsu ba.
Asali: Legit.ng
