Malaman Arewa Masu Adawa da Tinubu Sun Bullo, Sun Yi Gagarumin Gangami
- Malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa 19 su gudanar da taro na musamman domin nuna adawa da tazarcen shugaba Bola Tinubu
- Sun bayyana cewa sun yi taron ne bayan gudanar da cikakken nazari kan yadda shugaban kasar ya tafiyar da Najeriya daga 2023 zuwa yau
- Matakin na su ya zo a daidai lokacin da daraktan kamfen din Tinubu, Sanata Abdulaziz Yari ke neman hadin kan malamai game da zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa wasu malaman addinin Musulunci sun yi gangamin adawa da tazarcen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun bayyana cewa malamai akalla 1,000 ne suka taru a jihar Kano a ranar Lahadi, 4 ga Oktoban 2026 a wajen taron.

Kara karanta wannan
Kwana ya ƙare: Babban malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Yaakub ya rasu

Source: Facebook
Shekh Bashir Kabir Abdulhamid ne ya wallafa bidiyon matsayar malaman a wani sako da ya wallafa a Facebook.
Dalilin yin taron malaman
Sheikh Bashir Abdulhamid ya bayyana cewa bayan nazari da lura da abubuwan da suka faru a Najeriya, sun yanke taruwa domin yin matsaya.
A bayanin da ya yi, ya sanar da cewa malamai 1,000 ne daga jihohin Arewa suka hadu domin daukar matsayar siyasa a zaben 2027.
Abubuwan da aka cimma
A game da tattalin arziki, taron malaman ya nuna rashin amincewa da salon tafiyar da mulkin shugaba Ahmed Tinubu.
Taron ya ce manufofin tattalin arzikin shugaba Bola Tinubu kamar janye tallafin man fetur, sauya fasalin canza Naira da tallafin lantarki sun jefa talakawa a wahala.
Malaman sun ce ba za su goyi bayan shugaba Bola Tinubu ba matukar bai sauya manufofn da suka jefa al'ummar kasar a wahala ba.

Kara karanta wannan
Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Komawa Ƙarfi da Yaji
A kan tsaro kuma, taron malaman ya nuna damuwa kan yadda ake cigaba da kashe-kashe a fadin Najeriya a karkashin Bola Tinubu.
Saboda haka taron ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin kawo karshen matsalar, sun ce idan ba haka ba, ya kamata shugaban ya hakura da takarar 2027.
Sun ce idan shugaba Tinubu bai hakura da takarar 2027 ba, akwai bukatar talakawa su kauracewa zaben shi saboda matsalolin tsaro.

Source: Facebook
Sauran abubuwan suka fada
Malaman sun yi korafi kan yadda 'yan Najeriya ke yin tururuwa zuwa kasashen waje domin neman abinci, inda ta bukaci a kara albashi da sauransu.
Taron ya ja hankalin malaman Musulunci su kaucewa zama 'yan bangar siyasa saboda wani abu da za a iya ba su a lokacin kamfen.
A karshe, taron ya bukaci jama'a su zabi duk wanda zai kawo saukin rayuwa, walwala, aikin yi, cigaba ba tare da lura da jam'iyya ko kabila ba.
An nemi yi wa Rarara duka
A wani labarin, kun ji cewa mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya sha da kyar a wajen wani taro a Abuja game da tallata Bola Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu matasa ne suka yi kokarin lakadawa Rarara duka a lokacin da ya yi niyyar yi wakar yabon APC.
Lamarin ya faru ne a wajen taron ranar 'yancin kai da aka shirya a Abuja a ranar 1 ga Oktoba domin murnar cikar Najeriya shekara 66.
Asali: Legit.ng
