"Ban Tsani Kiristoci ba"; Sheikh Jingir Ya Yi Karin Haske kan Kalamansa

"Ban Tsani Kiristoci ba"; Sheikh Jingir Ya Yi Karin Haske kan Kalamansa

  • Sheikh Sani Yahaya Jingir ya musanta zargin cewa ba ya son Kiristoci, yana mai cewa an yi wa kalamansa mummunar fahimta
  • Shugaban na JIBWIS ya ce Musulunci ya koyar da soyayya da adalci ga mabiyan sauran addinai da mazhabobi
  • Ya kuma yi kira ga shugabannin Najeriya da su yi adalci ga kowa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Jos, Plateau - Shugaban Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya musanta zargin cewa ba ya son Kiristoci, yana mai cewa rahotannin da ke cewa haka “zargi ne kawai”.

Sheikh Jingir ya ce kalaman da ya yi a wajen bikin auren ma’aurata 1,500 da gwamnatin jihar Kano ta shirya ba su da nufin nuna ƙiyayya ga Kiristoci ko waɗanda ba Musulmi ba.

Kara karanta wannan

Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027

Jingir ya yi magana kan kalamansa
Sheikh Sani Yahaya Jingir na gabatar da jawabi Hoto: Garkuwan Sunnah
Source: Facebook

Sheikh Jingir ya bayyana matsayarsa

Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin dayake magana a wajen taron yini ɗaya wanda aka gudanar a Jos ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.

Sheikh Jingir ya bayyana cewa kalamansa ba su da nufin nuna ƙiyayya ga Kiristoci.

Hedikwatar ƙasa ta JIBWIS ce ta shirya taron domin wayar da kan mambobinta kan buƙatar shiga zaɓen da ke tafe cikin hikima.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da gwamnonin Yobe, Mai Mala Buni; Kano, Abba Kabir Yusuf; Jigawa, Umar Namadi; da Sokoto, Dr Ahmed Aliyu, na daga cikin waɗanda suka halarci taron.

Da yake magana, Sheikh Jingir ya ce:

“Mutane da yawa suna cewa ba na son Kiristoci. Ban ce ba na son Kiristoci ba. Ƙarya ce. An yi wa kalamaina mummunar fahimta. Shugabanci a Musulunci ba ya nufin yaudarar mutanen da ke da addini daban. Musulunci yana koyar da mu mu nuna soyayya ga mutanen da ke da addinai daban.”

Kara karanta wannan

Babban balilin da ya sa Amurka ba za ta cire Najeriya daga jerin kasashen CPC ba

Ya ambaci koyarwar Musulunci

Malamin ya ƙara bayyana cewa Musulunci ya jaddada cewa duk Musulmin da ya yaudari wanda ba Musulmi ba za a tambaye shi a Ranar Alƙiyama.

Ya kuma ce Annabi Muhammad (SAW) ya rayu cikin zaman lafiya da waɗanda ba Musulmi ba, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Da yake sake jaddada koyarwar Musulunci kan adalci a shugabanci, malamin ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu, gwamnoni da sauran shugabanni a dukkan matakai da su yi wa kowa adalci ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.

Wace shawara ya ba Tinubu?

“Ina kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya yaudari waɗanda ba Musulmi ba da Musulmi baki ɗaya. Haka kuma ina kira gare ku kada ku yaudari waɗanda ba sa cikin jam’iyyar siyasa ɗaya da ku ba. Ku yi shugabanci da adalci da gaskiya ga dukkan ’yan Najeriya,” in ji shi.

Ya jaddada cewa kowane ɗan Najeriya na da ’yancin zaɓar ɗan takarar da yake ganin ya dace da shi a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Trump ya fadi babban burin gwamnatinsa kan Iran

“Duk mutum yana da ’yancin zaɓar duk wanda yake ganin ya dace ya zaɓa a lokacin zaɓe,” in ji shi.
Jingir ya ce bai tsani Kiristoci ba
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir Hoto: Garkuwan Sunnah
Source: Facebook

Sheikh Jingir ya yi karin haske

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske kan goyon bayansa ga tikitin muslim-muslim.

Sheikh Jingir ya bayyana cewaya daɗe yana goyon bayan a samu shugaban ƙasa musulmi kuma mataimakinsa musulmi, tun kafin zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng