Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Bayanai kan Jirgin Saman Sojoji da Ya Yi Hatsari

Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Bayanai kan Jirgin Saman Sojoji da Ya Yi Hatsari

  • Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ya tabbatar da hatsarin wani jirgin sojoji dauke da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgi bakwai
  • Jirgin mai lambar rajista NGR 931 ya bace ne yayin da yake kan hanyar Benin zuwa Legas da misalin ƙarfe 9:13 na safe
  • An gano tarkacen jirgin kusa da sansanin sojojin ruwa na Igbokoda, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman waɗanda ke cikin jirgin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ondo - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Festus Keyamo, SAN, ya tabbatar da hatsarin wani jirgin soji a Igbokoda, jihar Ondo, wanda ke ɗauke da mutane 32.

Keyamo ya ce jirgin mai lambar rajista NGR 931 ya bace ne yayin da yake kan hanyar Benin zuwa Lagos da misalin ƙarfe 9:13 na safe.

Kara karanta wannan

Jirgin rundunar sojojin Najeriya ya yi hatsari, ana fargabar mutane da dama sun mutu

Jirgin sama ya yi hatsari a Ondo
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo Hoto: @fkeyamo
Source: Facebook

Jirgin ya bace bayan an daina jin duriyarsa

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Festus Keyamo ya sanya a shafinsa na X a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026.

A cikin sanarwar, ministan ya ce masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun sanar da hukumomi bayan sun kasa samun damar tuntuɓar jirgin ta rediyo.

A cewarsa, bayan samun ƙarin bayanai, an tabbatar da cewa jirgin sojojin ya yi hatsari ne a kusa da Sansanin Sojin Ruwa na Igbokoda, inda tuni aka gano tarkacen jirgin.

Festus Keyamo ya bayyana cewa jami’an ceto na ci gaba da gudanar da bincike da ƙoƙarin ceto waɗanda ke cikin jirgin.

Mutane 32 ne ke cikin jirgin

Keyamo ya bayyana cewa bayanan farko sun nuna cewa akwai mutane 32 a cikin jirgin.

“Bayanan farko sun nuna cewa fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgi bakwai ne ke cikin jirgin,” in ji ministan.

Kara karanta wannan

Sama da mutane 30 sun mutu da hatsarin jirgi ya rutsa da masu zuwa jana'iza a Najeriya

Wannan ya sa adadin mutanen da ke cikin jirgin lokacin da mummunan hatsarin ya auku ya kai mutum 32.

Keyamo ya bayyana iyakar alhakin ma’aikatarsa

Ministan ya fayyace cewa kula da zirga-zirga da tsarin gudanar da jiragen soji ba ya ƙarƙashin ikon Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ko Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).

Sai dai Keyamo ya ce ya tattauna da Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, kan lamarin.

Ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar za ta bayar da cikakken haɗin kai da taimako wajen aikin neman da ceto mutanen da ke cikin jirgin.

Ana jiran ƙarin bayani

Keyamo ya ce hukumomi za su fitar da ƙarin bayani kan hatsarin yayin da ake samun cikakkun bayanai.

“Za a samar da ƙarin bayani kan wannan mummunan lamari daga baya,” in ji ministan.
Sojojin sama sun rasa jirginsu a Ondo
Taswirar jihar Ondo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jirgin sojojin saman Amurka ya yi hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin yaƙin sojojin Amurka kirar F-16 Fighting Falcon ya yi hatsari a wani sansanin sojin Amurka da ke yammacin ƙasar Jamus.

Lamarin hatsarin wanda ya jikkata matuƙin jirgin ya​ auku ne a ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng