Atiku Abubakar zai Dawo da Tallafin Man Fetur idan Ya Ci Zaben 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027
- Ya ce gwamnati ta kasa fadin inda kuɗin da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur suka tafi, yana mai cewa ya kamata a yi amfani da su wajen rage talauci
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai dawo da tallafin tare da ƙwato kuɗin da ya ce an wawure, idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana shirin dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasara a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi ranar Laraba, inda ya ce ba ya adawa da cire tallafin man fetur, sai dai yana neman gwamnati ta bayyana inda kuɗin da aka samu suka tafi.

Source: Facebook
A wata hira da ya wallafa a Facebook, Atiku ya ce da an yi amfani da kuɗin wajen rage talauci, ilimi, tsaro da samar da damammaki ga matasa, da cire tallafin ya kasance mataki mai amfani.
Atiku zai dawo da tallafin mai
Atiku ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, zai dawo da tallafin man fetur, tare da ƙoƙarin ƙwato kuɗin da ya ce an sace.
Ya bayyana cewa:
“Ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma ina kuɗin? Ina aka kai su? An yi niyyar amfani da su wajen rage talauci da taimaka wa yara su samu ilimi. Ina kuɗin yanzu? Da alama kawai ana satar su ne.”
Ya ƙara da cewa idan ya zama shugaban ƙasa, zai dawo da tallafin, sannan duk wanda ya wawure kuɗin zai mayar da su.
Atiku ya ce cire tallafin man fetur zai iya zama mataki mai kyau idan an karkatar da kuɗin da aka samu zuwa ayyukan ci gaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Duk da shan wahala a zaɓen Osun, Davido ya faɗi yadda Tinubu zai yi nasara a 2027
Ya ce ya kamata a yi amfani da kuɗin wajen inganta tsaro, ilimi da samar da ayyukan yi da damammaki ga matasa.

Source: Getty Images
Tinubu ya cire tallafin mai
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur ne a jawabin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023.
Matakin ya haifar da ƙarin farashin man fetur, wanda ya kuma jawo tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.
Wasu gwamnonin jihohi sun bayyana cewa rabon kuɗaɗen da suke samu daga Asusun Tarayya (FAAC) ya ƙaru sosai tun bayan cire tallafin.
Gwamnati ta kare cire tallafin
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce matatar Dangote ba za ta iya fara aiki a ƙarƙashin tsarin tallafin man fetur ba.
Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin ya taimaka wajen samar da kasuwar da za ta bai wa masu zuba jari a matatun mai damar gudanar da kasuwancinsu.
Ya ce da an ci gaba da sayar da man fetur a farashin da aka tallafa na ƙasa da N200 kan kowace lita, Matatar Dangote ba za ta iya yin gogayya da man fetur da ake shigowa da shi ba.
Asali: Legit.ng
