An Shiga Tashin Hankali da Sabon Rikici Ya Barke a Taraba, Rayuka Sun Salwanta
- Akalla mutane bakwai sun mutu, yayin da aka kashe dabbobi 186 tare da kona gidaje sama da 340 a wani sabon rikici a Taraba
- Fiye da mutane 1,000 sun rasa matsugunansu, yayin da wasu mazauna yankin suka tsere zuwa Kamaru saboda fargabar ci gaba da rikicin
- Gwamnatin Taraba ta umarci jami’an tsaro su kama tare da gurfanar da duk wanda ke da hannu a rikicin ba tare da la’akari da matsayinsa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Wani sabon rikici tsakanin mazauna Mambilla da makiyayan Fulani ya yi sanadin mutuwar akalla mutane bakwai, kashe dabbobi 186 da kuma kona gidaje sama da 340 a jihar Taraba.
Lamarin ya faru a ƙauyukan Geroji da ke yankin Mbamnga, a Ƙaramar Hukumar Sardauna ta jihar, inda fiye da mutane 1,000 suka rasa matsugunansu.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin da shugabannin al’umma sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda har yanzu ba a san inda wasu da dama suka shiga ba.
Rikicin ya samo asali daga saɓani
Majiyoyi sun ce rikicin ya ɓarke ne a daren Juma’ar da ta gabata bayan wata takaddama tsakanin wata mata ‘yar Mambilla da wani Bafillatani.
Daga bisani rikicin ya yaɗu zuwa al’ummomin Geroji da Mbara, da kuma wasu ƙauyuka da suka haɗa da Wuro Buba, Wuro Ardo Bashiru, Wuro Wakili Idrisa da Wuro Saleh Petel.
Sauran wuraren da lamarin ya shafa sun haɗa da Wuro Hassan Jaji, Wuro Alhaji Jibo, Wuro Alhaji Manu da Wuro Mbarkal.
Daya daga cikin shugabannin al’umma, Ardo Bashiru, ya ce sun rasa kusan komai sakamakon rikicin.
Wasu mutane sun tsere zuwa Kamaru
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce daruruwan mazauna yankin, ciki har da mata da yara, sun tsere daga ƙauyukan zuwa Jamhuriyar Kamaru domin neman mafaka.
A cewarsa, mutanen sun tsallaka zuwa Nyang da ke yankin Donga-Mantung, bayan wani rukunin mutane da ba a tantance su ba ya shiga ƙauyen tare da harbin mazauna da kuma cinna wa gine-gine wuta.
An tura jami’an tsaro yankin
Shugaban Ƙaramar Hukumar Sardauna, Alhaji Mohammed Umar, ya tabbatar da cewa mutane da dama sun tsere daga yankin.
Ya ce ana shirye-shiryen dawo da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu, yayin da aka tura jami’an tsaro yankin da abin ya shafa.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce gwamnatin jihar ta ƙara yawan jami’an sojoji da ’yan sanda domin hana rikicin yaɗuwa zuwa wasu wurare.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya, ƙungiyoyin agaji da kuma ƙasashen duniya da su gaggauta bayar da tallafi domin sake tsugunar da waɗanda abin ya shafa da kuma farfaɗo da rayuwarsu.
Gwamna ya umarci kama waɗanda suka haddasa rikicin
Domin dawo da doka da oda bayan rikicin, Gwamnan Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana da hannu a rikicin.
Gwamnan ya jaddada cewa babu wanda za a kare daga hukuncin doka saboda matsayinsa na zamantakewa ko na siyasa.

Kara karanta wannan
Iska mai ƙarfi ta haddasa hatsarin jirgi, mata da dama sun rasa rayukansu a Najeriya
Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Taraba (SSG), Chief Gebon Timothy Kataps, ne ya bayyana umarnin a cikin wata sanarwa.
A halin da ake ciki, Sakataren Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Jihar Taraba (SEMA), Echuseh Audu, ya sanar da tura kayan agaji ga iyalan da abin ya shafa.
Kayan agajin sun ƙunshi abinci, magunguna da kayan samar da matsuguni na wucin gadi, waɗanda hukumar ta ce za a raba su cikin sa’o’i 48 na farko.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe mataimakin kwamanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kashe Mataimakin Kwamandan Operation Rainbow, CSP Dennis David Babale.
'Yan bindigan sun kashe mataimakin kwamandan ne bayan sun yi wa jami’an rundunar kwanton bauna a hanyar Bokkos zuwa Barkin Ladi da ke jihar Plateau.
Asali: Legit.ng

