Saura Kwana 100 Zabe: INEC za Ta Yi wa 'Yan Najeriya Bayani kan 2027
- Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, za ta yi wa ’yan Najeriya bayani kan shirye-shiryenta yayin da aka shiga kwanaki 100 kafin babban zaben 2027
- Hukumar za ta mayar da hankali kan rajistar masu kada kuri’a, tantance ’yan takara, harkokin sufuri da sauran matakan da ake dauka domin tabbatar da sahihancin tsarin zaben
- Taron masu ruwa da tsaki da taron manema labaran zai gudana ne a Abuja ranar Talata, 6 ga Oktoba, inda shugaban INEC, Joash Amupitan, zai yi jawabi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, za ta yi wa ’yan Najeriya bayani kan matakin da ta kai na shirye-shiryen babban zaben 2027 yayin da ake shiga kwanaki 100 kafin fara kada kuri’a.

Kara karanta wannan
Babbar magana: An yi yunkurin kashe ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Najeriya
Hukumar ta shirya gudanar da taron masu ruwa da tsaki na kasa da kuma taron manema labarai na duniya ranar Talata, 6 ga Oktoba, a Abuja.

Source: Twitter
INEC za ta yi bayani
Punch ta rahoto cewa INEC ta ce taron zai mayar da hankali kan muhimman bangarorin shirye-shiryen zaben, ciki har da rajistar masu kada kuri’a, gabatar da sunayen ’yan takara, harkokin sufuri da matakan kare sahihancin tsarin zaben.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, SAN, zai yi jawabi a wajen taron tare da sauran masu ruwa da tsaki da ke da hannu a harkokin zabe.
Hukumar ta ce taron zai ba ’yan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki damar fahimtar matakin da aka kai wajen shirye-shiryen babban zaben na 2027.
Masu ruwa da tsaki za su halarta
INEC ta ce shugabannin jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro da ke cikin Kwamitin Tuntuba kan Tsaron Zabe, jami’an diflomasiyya, kungiyoyin farar hula da masu sa ido kan zabe na daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron.
Haka kuma, ana sa ran masu rajin kare hakkin masu bukata ta musamman, shugabannin addinai da na gargajiya, kungiyoyin matasa da manyan jami’an kafafen yada labarai za su kasance a wajen taron.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa INEC ta ce ana shirya taron ne domin karfafa hadin gwiwa da sadarwa tsakanin hukumar da kungiyoyi da hukumomin da ke da muhimmiyar rawa wajen gudanar da zabe.
Taron zai gudana a Abuja
An shirya gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Kasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, da karfe 10:00 na safe ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026.
Hukumar ta ce shiga wajen taron zai kasance ne bisa gayyata kawai, yayin da ’yan jarida da aka amince da su da sauran baki za su bukaci nuna katin gayyata ko alamar tantancewa a wuraren binciken jami’an tsaro.
INEC ta kuma ce za a watsa taron kai tsaye ta manyan tashoshin talabijin na kasa, sannan a yada shi ta shafukanta na sada zumunta domin ba ’yan Najeriya da dama damar bibiyar abin da ake tattaunawa.
INEC za ta dauki aiki

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: INEC ta shirya sanar da makomar takarar Sheikh Pantami a zaben 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta bude shafinta na daukar ma’aikatan wucin gadi da za su taimaka wajen gudanar da babban zaben 2027.
Hukumar ta ce shafin INECPRES ya fara aiki ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026, domin wadanda suka cancanta su nemi aikin ma’aikatan zabe na wucin gadi.
INEC ta bayyana cewa shafin zai kasance a bude har zuwa tsakar daren Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, inda masu sha’awar aikin za su iya amfani da shafin da hukumar ta ware domin yin rajista.
Asali: Legit.ng
