Duk da Gwamna Ya Sanya Doka, An Kashe Malamin Addini da Wasu Mutane Sama da 20
- An kashe Fasto Samuel Nandi da wasu mutane 27 a hare-haren da aka kai sassan Jihar Plateau cikin mako guda
- Hare-haren sun faru tsakanin 13 zuwa 20 ga Satumba a kananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos, Mangu, Riyom da Jos South
- Kashe-kashen da ke yi a yankunan ya ci gaba duk da dokar hana fita daga magariba zuwa safiya da gwamnatin jihar ta kakaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - An kashe malamin coci da wasu mutane 27 a hare-haren da aka kai sassan Jihar Plateau cikin mako guda.
Wannan kashe-kashen rayuka ya faru ne duk da dokar hana fita daga magariba zuwa safiya da gwamnatin jihar Filato ta kakaba domin dakile tashin hankalin.

Source: Original
A rahoton Leadership, kungiyar kiristoci ta ICC ta ce an kashe mutanen ne tsakanin 13 zuwa 20 ga Satumba, 2026 a wasu garuruwa da ke kananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos, Mangu, Riyom da Jos South.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
An kashe malamin coci a Filato
ICC ta rawaito David Nanpet, wani mai rubuta rahotannin gani da ido na kungiyar ICON, yana tabbatar da kisan Fasto Samuel Nandi yayin da yake tafiya zuwa ibadar coci a Maraban Kantoma, Karamar Hukumar Barkin Ladi, ranar Lahadi, 20 ga Satumba.
Nanpet ya shaida wa ICC cewa an ci gaba da jin karar harbe-harbe a Maraban Kantoma, Rapwomol da Shurum bayan kashe faston.
“Faston yana kan hanyarsa ta zuwa coci. Sun kai masa hari kuma suka kashe shi,” in ji Nanpet kamar yadda aka rawaito.
Mai rubuta rahotannin gani da ido ya kuma bayar da rahoton abin da ya bayyana a matsayin yiwuwar amfani da jirgi mara matuki wajen leken asiri a kusa da kauyen Darwat.
“An ga wani jirgi mara matuki yana leken asiri a Darwat a wannan daren,” in ji Nanpet.
Mahara sun kashe mutane 27
Ya kara da cewa mazauna yankin na fargabar cewa na’urar na iya kasancewa tana da alaka da kungiyoyin yan ta'adda masu dauke da makamai da ke shirin kai hari.

Kara karanta wannan
Sama da mutane 30 sun mutu da hatsarin jirgi ya rutsa da masu zuwa jana'iza a Najeriya
Ya ce an jibge motar yaki mai sulke a cikin al’ummar, lamarin da ya sa shiga wurin kai tsaye ke da wahala, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
A cewar ICC, an kashe akalla wasu mutane 27 a hare-haren da aka kai a sassan yankin da abin ya shafa cikin kwanaki bakwai.

Source: Facebook
An dokar zaman gida a wasu yankuna
Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya kakaba dokar hana fita daga magariba zuwa safiya a kananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos da Mangu.
Gwamnatin jihar ta ce dokar ta fara aiki ne ranar Litinin, 21 ga Satumba, kuma za ta kasance daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kullum har sai an ba da wata sabuwar sanarwa.
An kashe mutane 10 a Barkin Ladi
Kun ji cewa adadin mutanen da aka kashe a hare-haren da aka kai wa yankunan ƙaramar hukumar Barkin Ladi ya kai 10, ciki har da ɗan sanda ɗaya.
Maharan sun kai hare-haren ne a lokaci guda a yankunan Sabon Layi, Rakung, Gangare, da kuma kusa da babban asibitin garin Barkin Ladi.
Asali: Legit.ng