Christopher Musa: An Bukaci Ministan Tsaro Ya Yi Murabus, an Ji Dalili

Christopher Musa: An Bukaci Ministan Tsaro Ya Yi Murabus, an Ji Dalili

  • MURIC ta ce an kashe mutane 43 da limami, sannan aka sace wasu 19 a jihar Sokoto cikin makonni uku
  • Ƙungiyar ta zargi Sojojin Najeriya da gazawar kare al’ummar jihar tare da neman a samar da ingantaccen tsarin tsaro
  • MURIC ta bukaci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya kawo sauyi ko ya gabatar da takardar murabus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Ikeja, Jihar Legas - Ƙungiyar kare haƙƙin ta Musulmai, Muslim Rights Concern (MURIC), ta aika da sakon gargadi a Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya.

Kungiyar MURIC ta ba Ministan tsaron wa’adin kwanaki 14 domin ya nuna gagarumin sauyi a harkar tsaro a jihar Sokoto ko ya sauka daga mukaminsa.

An bukaci Christopher Musa ya yi murabus
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

A cewar rahoton Leadership, MURIC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, wadda Daraktan zartarwa na ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara, sun tura yan bindiga da dama lahira

Ƙungiyar ta ce Ministan ya gaza cika alkawarin da ya yi lokacin da ya fara aiki na kawo ƙarshen kashe-kashe da matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

An kashe mutane 44 a Sokoto cikin makonni 3

MURIC ta ce aƙalla mutane 43 da wani limami ne aka kashe a jihar Sokoto cikin makonni uku da suka gabata, yayin da wasu mutane 19 kuma aka yi garkuwa da su a cikin wannan lokaci.

Ƙungiyar ta ce dukkan waɗanda lamarin ya rutsa da su Musulmai ne, tare da bayyana hare-haren a matsayin barazana ga abin da ta kira cibiyar Musulunci a Najeriya.

Akintola ya ce idan Abuja ce cibiyar siyasar Najeriya, sannan Legas ce cibiyar tattalin arzikin ƙasar, to Sokoto ita ce zuciyar Musulunci a Najeriya.

Ya ce saboda muhimmancin jihar ga Musulman Najeriya, duk wani hari da aka kai Sokoto ana kallonsa a matsayin hari kan Musulmi baki ɗaya.

MURIC ta ɗora alhakin gazawar tsaro kai tsaye kan Rundunar Sojin Najeriya, tare da neman a samar da wani tsari mai ƙarfi na kare jihar Sokoto da yankunan da ke kewaye da ita.

Kara karanta wannan

DSS ta bankado shirin 'yan bindiga na kai hari manyan makarantu a Sokoto

Gargadin DSS ya kara daga hankalin MURIC

Ƙungiyar ta kuma yi nuni da wani gargadi da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayar na cewa ƴan ta’adda na shirin kai hare-hare kan manyan makarantun jihar Sokoto.

MURIC ta bayyana wannan gargadin a matsayin abin da ya sa ta yanke shawarar ɗaukar mataki kan lamarin.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Ministan Tsaro ya karya alkawarin da ya yi na kawo ƙarshen kashe-kashe. Ya gaza wa mutanen Sokoto. Ya gaza wa ’yan Najeriya.”

An bukaci a kare Sokoto sosai

MURIC ta tuno da kalaman da Musa ya yi lokacin da ya fara aiki, inda ya ce ya san ba zai iya bari ya gaza wa kansa, ƙasarsa da iyalinsa ba.

Sai dai ƙungiyar ta ce yadda al’amura suka kasance a ƙarƙashin jagorancinsa ya saba da wannan alƙawarin.

MURIC ta ce wa’adin kwanaki 14 zai fara ne daga Litinin, 24 ga Agusta, 2026, inda take buƙatar ganin sauye-sauye bayyanannu kuma za a iya tabbatar da su a tsarin tsaro na Sokoto da yankunan da ke kusa da jihar.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

An bukaci a kare Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ƙungiyar ta jaddada cewa dole ne a mayar da birnin Sokoto “wuri mai matuƙar wahalar kutsawa da kai hari”, tare da cewa bai kamata a bar wata barazana ta kusanci fadar Sarkin Musulmi ba.

MURIC ta ce idan Ministan ya gaza cika waɗannan buƙatun cikin wa’adin, abin da ya rage masa shi ne ya gabatar da takardar murabus ɗinsa kafin wa’adin ya ƙare.

Christopher Musa ya ba sojoji umarni

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya umarci jami'an tsaro da kada su yi kasa a gwiwa wajen hallaka 'yan bindiga da 'yan ta'adda

Janar Musa ya yi gargadi mai kaushi cewa duk jami'in da ya ki daukar mataki da sunan jiran umarni za a dauke shi tamkar mai hada baki da miyagun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng