Da Gaske ne: Trump Ya Tabbatar da Fargabar Harin Iran, Ya Yi Basaja a cikin Jirgi

Da Gaske ne: Trump Ya Tabbatar da Fargabar Harin Iran, Ya Yi Basaja a cikin Jirgi

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun sauya jirginsa a asirce saboda tsaro
  • An kawo rahoto cewa hukumomin Amurka sun gano sahihiyar barazanar Iran ta kai wa jirgin shugaban hari, lamarin da ya sa aka mayar da shi wani jirgin soja
  • Trump ya ce bai nemi cikakken bayani kan barazanar ba, yana mai cewa yana fuskantar barazana da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da rahoton da ake yadawa bayan zuwansa Turkiyya.

Trump ya tabbatar da cewa ya sauya jirgi a asirce bayan ya bar taron kungiyar NATO a Turkiyya.

Trump ya tabbatar da basaja a cikin jirgi
Shugaba Donald Trump na Amurka da Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Trump ya ce jami’an Hukumar Tsaron Sirri da sojojin Amurka ne suka umarce shi da ya yi amfani da wani jirgi daban yayin barin Ankara, cewar BBC.

Kara karanta wannan

Yadda barazanar Iran ta firgita Trump, ya sauya jirgi saboda tsoron kashe shi

Ya ce:

“Ina bin umarnin Hukumar Tsaron Sirri da sojoji. Sun so in shiga wani jirgi daban, don haka dole ne in yi abin da suka ce.”

Wannan bayani ya biyo bayan rahotannin cewa Trump ya fara shiga tsohon jirgin Air Force One, yayin da kyamarorin talabijin ke daukar hotonsa.

Rahotanni sun ce daga bisani an fitar da Trump daga jirgin shugaban ta wata motar kayan abinci da aka daga har zuwa kofar jirgin.

Hakan ya ba shi damar fita ba tare da ‘yan jarida da sauran fasinjoji sun gan shi ba, kafin a mayar da shi wani karamin jirgin soja.

Jami’an Amurka sun shaida wa CBS News cewa hukumomi sun gano wata sahihiyar barazanar Iran ta harba makami mai linzami kan jirgin.

Jaridar New York Times ta kuma ruwaito cewa leken asirin Amurka ya samu bayanan wani mutum kusa da taron NATO, wanda aka gan shi dauke da makami mai linzami.

Kara karanta wannan

Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Trump ya nuna cewa jirgin daban da ya shiga na iya kasancewa shi ma cikin hadari fiye da jirgin farko.

Shugaban ya ce bai nemi cikakken bayani game da barazanar ba, yana mai cewa kullum yana samun barazanar kashe shi.

Ya ce:

“Yana iya kasancewa cikin hadari mafi girma, domin ina ganin wannan shi ne jirgin da za a fi son kai wa hari.
“Ina tsammanin akwai wata barazana a can. Ban tambayi cikakken bayani ba. Ina samun barazana da yawa, ina samun barazana da yawa da ba ku sani ba.”

Trump ya isa Turkiyya ne da sabon jirgin Boeing 747-8 da Qatar ta ba Amurka, amma ya sanar da komawa da tsohon Air Force One.

Ya ce zai yi hakan ne “saboda tsohon lokaci”, inda aka dauki hotonsa yana shiga jirgin shugaban a filin jirgin Ankara ranar 8 ga Yuli.

Sai dai jaridar Washington Post ta ce daga baya Trump ya fita daga jirgin ta wata motar kayan abinci da aka ajiye a dayan gefen jirgin.

Daga nan motar ta kai shi wani jirgin soja kirar C-32A, wanda aka sauya daga Boeing 757 kuma manyan jami’an Amurka, ciki har da mataimakin shugaban kasa, ke amfani da shi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Yadda Trump ya tsara 'guduwa' daga yakin da ya ke da Iran

An ce Sakataren Tsaro Pete Hegseth ya shiga C-32A daban ta matakalar waje, abin da ya taimaka wajen nuna cewa sauyin jirgin na yau da kullum ne.

Trump ya magantu kan mashigar Hormuz

An ji cewa Donald Trump da ke matsayin shugaban kasar Amurka, ya bayyana kasar da ke da cikakken iko kan mashigar Hormuz.

Shugana Donald Trump ya ce ba ya yarda da Iran, yana zargin kasar da yi masa ƙarya da karairayi akai-akai.

Mohsen Rezaei ya ce ba za a sake buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta sauya halayenta kuma ta amince da sharuɗɗan Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.