Akpabio Ya Fadi Wanda ke Juya Najeriya yayin da Tinubu da Shettima ke Ketare

Akpabio Ya Fadi Wanda ke Juya Najeriya yayin da Tinubu da Shettima ke Ketare

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan rashin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a Najeriya
  • Akpabio ya ce babu wani gibi a fadar shugaban ƙasa, yana mai cewa Tinubu har yanzu shi ne ke jagorantar harkokin ƙasar duk da kasancewarsa a ketare
  • Kalaman Akpabio sun zo ne bayan wasu ’yan adawa sun yi tambayoyi kan wanda ke amfani da ikon shugaban ƙasa yayin da Tinubu da Shettima ba sa Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ba shi ne Mukaddashin Shugaban Ƙasar Najeriya ba duk da rashin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a ƙasar.

Akpabio ya bayyana hakan ne ranar Talata a wani taro a Ikot Ekpene da ke Jihar Akwa Ibom, yayin da ake ci gaba da muhawara kan rashin shugabannin biyu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Shugaba Tinubu da Kashim Shettima sun karya dokar Najeriya a lokaci 1

Sanata Godswill Akpabio
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Akpabio ya zama shugaban riko?

Daily Trust ta wallafa cewa Akpabio ya ce babu wani gibi a fadar shugaban ƙasa, yana mai cewa Tinubu har yanzu yana kan mulki kuma yana gudanar da harkokin Najeriya.

Ya ce:

“Ina son in gyara wata fahimta. Ni ne Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Majalisar Ƙasa. Da yardar Allah da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ba ni ne Mukaddashin Shugaban Ƙasa ba, domin Shugaban Ƙasa har yanzu yana kan mulki.”

Akpabio ya bayyana tafiyar Tinubu a matsayin hutun aiki, yana mai cewa abubuwan da shugaban ba zai iya yi daga Najeriya yana iya gudanar da su daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Da gaske ne mataimakin gwamna ya ce a yi wa Tinubu ruwan duwatsu?

'Babu gibi a fadar shugaban ƙasa'

Punch ta wallafa cewa shugaban Majalisar Dattawan ya ce Tinubu na ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati duk da kasancewarsa a ƙasashen waje.

Ya kawo misalin ganawar shugaban da Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yana mai cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu.

Ya kuma ce tun da Tinubu bai samu damar halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, UNGA, a New York ba, sai Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi.

Akpabio ya ce:

“Babu wani gibi. Mutanen da suke magana suna magana ne kawai. Ni ne mutum ɗaya tilo da nake matsayin Shugaban Majalisar Ƙasa da zan iya bayyana matsayar Majalisar Ƙasa kan ko akwai gibi ko babu.”

Ya ƙara da cewa Tinubu har yanzu yana gudanar da harkokin Najeriya, yana mai cewa ci gaban fasaha ya sa shugaban ƙasa zai iya bayar da umarni daga duk inda yake.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tinubu ya aika saƙo da aka sanar da rasuwar tsohon gwamna a Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kalaman Akpabio sun biyo bayan kiraye-kirayen da wasu ’yan adawa suka yi kan rashin Tinubu da Shettima a Najeriya a lokaci guda.

Wike ya magantu kan majalisa

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai goyi bayan Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ba bayan zaɓen 2027.

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya zargi Uzodimma da neman tasiri kan zaɓen ’yan majalisar da za su iya mara wa burinsa na zama Shugaban Majalisar Dattawa baya.

Wike ya ce wa’adin Uzodimma na gwamna zai ƙare a watan Janairun 2028, amma ya ce gwamnan na son barin kujerar domin neman shiga Majalisar Dattawa da kuma neman shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng