Kifar da Tinubu: Yadda aka ba Malamin Musulunci N10m a Yunkurin Juyin Mulki

Kifar da Tinubu: Yadda aka ba Malamin Musulunci N10m a Yunkurin Juyin Mulki

  • An gurfanar da daya daga cikin malaman Musulunci, Sheikh Bukar Kashim Goni da ake zargi da hannu a yunkurin yi wa Bola Ahmed Tinubu juyin mulki
  • A zaman kotun da aka yi, Sheikh Bukar Goni ya tabbatar da cewa daya daga cikin wanda ake zargi da yunkuirin kifar da gwamnati ya tura masa kudi
  • Sai dai malamin ya yi karin haske game da tura masa kudin, inda ya ki yarda da cewa yana da hannu a cikin yunkurin kifar da shugaba Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Bukar Kashim Goni da ake zargi da hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar juyin mulki ya yi bayani.

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya ce an ba shi sama da Naira miliyan 10 da aka tura a asusun bankinsa ne domin addu’o’i.

Kara karanta wannan

Trump ya ja da baya kan shirin gwabzawa da dakarun Iran a Hormuz

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu na sauraron jawabi a Aso Villa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Yadda aka yi zaman shari'ar juyin mulki

Vanguard ta wallafa cewa a zaman da aka yi ranar Talata, kotun da Mai shari’a Joyce Abdulmalik ke jagoranta ta kalli bidiyon shaida da ke nuna tattaunawar da malamin ya yi da jami’an tsaro da suka binciki lamarin.

Lokacin da masu bincike suka fuskance shi da cewa an tura masa makudan kuɗi da ake zargin suna da alaƙa da wanda ake zargi, Kanal Mohammed Ma’aji, nan take ya musanta duk wata alaƙa da shirin kifar da gwamnatin Tinubu.

Rahoto ya nuna cewa Sheikh Goni ya jaddada cewa dukkan kuɗin da ya karɓa daga Kanal Ma’aji an ba shi ne kawai domin addu’o’i da ayyukan alheri.

A cewar wani rahoto da the Sun ta wallafa ya ce jami’in sojan ya nemi addu’a ne saboda jinkirin karin girma da wasu matsalolin rayuwa.

Yadda aka yi zaman kotu kanzargin kifar da Bola Tinubu
Sashen mahalarta zaman kotu kan shari'ar yunkurin juyin mulki a Abuja. Hoto: Sadeesu Sufi Attijjani
Source: Facebook

Yadda aka turawa malamin kudi

Masu bincike sun kalubalanci bayaninsa da hujjoji daga bayanan asusun bankinsa, inda aka nuna cewa an fara tura masa kuɗi tun watan Maris 2023, watanni kafin matsalar karin girman da ya ambata.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama ma'aikaci a fadar Aso Rock kan zargin yunkurin juyin mulki

Haka kuma, sun nuna masa wasu mu’amaloli da suka kai miliyoyin Naira, ciki har da tura Naira miliyan 10 da aka ce an yi masa a watan Oktoba 2024.

An kuma tambaye shi yadda wasu tattaunawarsa da babban wanda ake zargi suka haɗa da kalmomi irin su “samun dama” da “kayan aiki,” wanda masu bincike suka ce na nuni da wani babban shiri kamar juyin mulki.

Sai dai Sheikh Goni ya nace a kan matsayarsa, yana mai cewa bai san da wani shiri na hakam ba, kuma ba shi da wata alaƙa da harkokin siyasa ko soja.

An kama ma'aikacin Aso Villa

A wani labarin, mun kawo muku cewa an kama wani daga cikin ma'aikatan fadar shugaban kasa, Zekari Umoru kan yunkurin juyin mulki.

A bayanan da Zekari Umoru ya yi, ya sanar da cewa wani ne da ke aiki a fadar shugaban kasa ya hada shi da wani jami'in sojan Najeriya suka fara alaka.

A wani bidiyo da aka nuna a kotu, an ga Umoru ya ce an yaudare shi ne ya shiga hulɗa da Kanal Ma’aji da ya ba shi makudan kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng