Dangote Ya Waiwayi Mata, Ya Yi Masu Tanadi na Musamman a Matatarsa

Dangote Ya Waiwayi Mata, Ya Yi Masu Tanadi na Musamman a Matatarsa

  • Aliko Dangote ya ce Gidauniyar Aliko Dangote za ta haɗa gwiwa da gwamnatocin jihohi domin taimaka wa mata masu rauni kusan miliyan biyu su sayi hannun jari a matatar Dangote
  • Shirin zai fi mayar da hankali kan zawarawa, waɗanda rikice-rikice suka shafa da sauran mata masu fuskantar matsalar tattalin arziki
  • Gidauniyar ta ce za ta ƙara ba matan da suka sayi hannun jari wasu hannun jari kyauta domin su riƙe su a matsayin ajiyar kuɗi na dogon lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana tanadin da ya yi wa mata masu karamin karfi a matatarsa.

Dangote ya ce gidauniyar Aliko Dangote za ta haɗa gwiwa da gwamnatocin jihohi domin taimaka wa kusan mata miliyan biyu masu rauni su mallaki hannun jari a matatarsa.

Kara karanta wannan

Da gaske ne mataimakin gwamna ya ce a yi wa Tinubu ruwan duwatsu?

Dangote zai taimaka wa mata
Aliko Damgote na jawabi a wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya bayyana hakan ne a New York yayin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81, cewar rahoton jaridar The Punch.

Ya fadi hakan ne bayan da Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dakta Goje Mohammed, ya tambaye shi yadda haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wa al’ummomin da rikice-rikice suka shafa.

Zawarawa za su samu damar mallakar hannun jari

Dangote ya ce gidauniyar za ta yi aiki tare da gwamnatocin jihohi domin bai wa zawarawa, waɗanda rikice-rikice suka shafa da sauran mata masu rauni damar shiga shirin sayen hannun jari na matatar.

“Za mu haɗa gwiwa da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da cewa zawarawa da sauran mata masu rauni sun samu damar sayen hannun jari a matatar,” in ji Dangote.

Ya ce shirin ba zai tsaya kan taimaka wa matan su sayi hannun jari kawai ba, jaridar Daily Trust ta dauko labarin.

Gidauniyar za ta ƙara ba su hannun jari

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Dangote ya ce gidauniyar za ta kuma ba matan da suka saka hannun jari ƙarin hannun jari kyauta, domin su riƙe shi a matsayin ajiyar kuɗi na dogon lokaci.

“Baya ga taimaka musu su sayi hannun jari, gidauniyar za ta kuma tallafa musu ta hanyar ba su ƙarin hannun jari da za su riƙe a matsayin ajiyar kuɗi domin gaba.
“Manufarmu ita ce mu kai ga kusan mata miliyan biyu ta wannan shiri,” ya ƙara da cewa.

Shirin ‘People’s IPO’ na Dangote

Shirin na daga cikin babban tsarin “People’s IPO” na Matatar Dangote, wanda ke da nufin faɗaɗa damar ’yan Najeriya su mallaki wani kaso na matatar mai ta hanyar sayen hannun jari. Matatar tana da ƙarfin tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana.

Ana sa ran haɗin gwiwar zai fi mayar da hankali kan mata masu rauni a al’ummomin da rikice-rikice suka shafa, musamman zawarawa da iyalan da ke fuskantar matsin tattalin arziki.

A tsarin da ake shirin aiwatarwa, gwamnatocin jihohi da gidauniyar za su taimaka wa matan da suka cancanta wajen samun damar shiga shirin sayen hannun jarin.

Kara karanta wannan

"Ku nemi mafaka," NiHSA ta jero jihohi 15 da za a yi mummunar ambaliyar ruwa a Najeriya

Ƙarin hannun jarin da gidauniyar za ta bayar kuma zai samar wa waɗanda suka amfana da wata kadarar kuɗi da za su iya riƙewa na dogon lokaci.

Mata za su samu dama a matatar Dangote
Hamshakin attajiri, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shawarar Sanusi II kan hannun jarin matatar Dangote

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan sayen hannun jari a matatar Dangote.

Sanusi II ya shawarci masu shirin saka jari da kada su yi amfani da muhimman kuɗaɗen tafiyar da rayuwa, kamar kuɗin makarantar ’ya’yansu ko gidajen da suke zaune, wajen sayen hannun jari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng