Sheikh Sani Khalifa Ya Amayar da Abin da Ya Sani kan Shirin Juyin Mulki a Gaban Kotu
- Babban malamin musulunci a Zaria, Sheikh Sani Khalifa ya gabatar da bayani kan zargin da ake masa na hannu a shirin juyin mulki
- Bayanin malamin na cikin wani faifan bidiyo da bangaren gwamnatin tarayya ya gabatar a zaman babbar kotun tarayya
- Malamim ya tabbatar da cewa an tuntube shi domin ya yi addu'a ga masu shirin juyin mulki, amma ya gargade su da cewa ba za su yi nasara ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Malamin addinin Musulunci da ke fuskantar shari’a kan zargin hannu a shirya juyin mulki, Sheikh Sani Abdulkadir, ya yi wa kotu bayani.
Malamin ya shaida wa kotu cewa tun farko ya gargadi wadanda suka kitsa yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu juyin mulki cewa ba za su yi nasara ba.

Source: Facebook
Vangaurd ta ce Sheikh Sani Khalifa ya bayyana hakan ne ranar Litinin a cikin wani faifan bidiyo da masu gabatar da kara suka mika wa babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Malamin ya ce an tuntube shi ne domin ya yi addu’o’i da za su hana bayanan sirrin shirin juyin mulkin su fita waje.
An gabatar da bidiyon Sheikh Sani Khalifa
A cikin bidiyon da aka nuna a zaman kotu, shehin malamin ya ce bai dade da sanin jagoran shirin ba, Kanal Mohammed Ma’aji, inda ya ce dhi ke aiko wani mai suna Sanda domi a taimaka masu da addu'a.
A cewarsa, Sanda ya gaya masa cewa “ogansa” na son kifar da gwamnati kuma suna bukatar addu’a da duba domin sanin ko shirin zai yi nasara.
Limamin ya ce bayan ya gudanar da addu’o’i, ya sanar da su cewa shirin ba zai yi nasara ba, sannan mutane biyu daga cikinsu za su tona asirin sauran.

Kara karanta wannan
"Ba a fahimce ni ba," Ganduje ya bayyana dalilin kiran Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
Da gaske an turawa malamin kudi?
Sheikh Sani Khalifa ya bayyana cewa daga baya an rika turo masa kudi domin addu’a da sadaka, tare da sunayen mutanen da ake zargin suna cikin shirin domin a saka su cikin addu’o’in.
Ya ce bayan an fara addu’o’in ne Sanda ya sanar da shi cewa an daina ganin Kanal Ma’aji na tsawon kwanaki hudu, kafin daga bisani ya ji ta kafafen yada labarai cewa an kama wasu mutane kan zargin kitsa juyin mulki.
Limamin ya dage cewa kudin da aka tura masa ba domin tallafawa juyin mulki ba ne, illa domin yin addu’a.
Da masu bincike suka tambaye shi abin da ya fahimta da juyin mulki, Malamin ya ce yana nufin sojoji su karbe gwamnati da karfin bindiga.
Abin da ya hana malamin kai rahoto
Kan dalilin da ya sa bai kai rahoton lamarin ga hukumomi ba, ya ce bai san wanda zai kai wa rahoton ba ne.
Ya kuma bayyana cewa an kama shi ne bayan ya je hukumar EFCC saboda an sanya takunkumi a asusun ajiyarsa na banki.
Lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo SAN, ya bukaci kotu ta karbi rubutattun bayanan da wadanda ake tuhuma suka bayar ga kwamitin bincike na musamman da aka kafa.

Source: Twitter
Sai dai lauyoyin wadanda ake tuhuma sun ki amincewa da karbar bayanan da bidiyoyin, suna masu cewa ba da son ran wadanda suke karewa aka karbi bayanan ba.
Sun bukaci a gudanar da abin da ake kira trial-within-trial domin tantance ko an bayar da bayanan da son rai ko akasin haka.
Mai Shari’a Abdulmalik ta amince da bukatar tare da dage cigaba da shari’ar zuwa ranar 12 ga Mayu, 226 da karfe 12 na rana, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ma'aikacin Aso Rock ya yi bayani
An ji cewa wani ma’aikacin kamfanin Julius Berger da ke aiki a sashen kula da gyare-gyare na fadar shugaban ƙasa ya yi magana kan zargin juyin mulki.
Mutumin mai suna Zekari Umoru, ya ce an ruɗe shi har aka sanya shi a cikin shirin juyin mulki inda ya ce ya yi nadama matuka.
Umoru, wanda shi ne mutum na huɗu cikin waɗanda ake tuhuma, ya bayyana cewa ya haɗu da wasu daga cikin waɗanda ake zargi ne ta hannun Ahmed Ibrahim
Asali: Legit.ng

