Farashin Mai Ya Ruguzo Kasa bayan Trump da Iran Sun Fahimci Juna
- Farashin danyen mai ya ragu a kasuwannin duniya bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ce jami’an Amurka da Iran sun gudanar da tattaunawa mai kyau
- Farashin Brent da WTI ya koma kasa da dala 100 kan ganga, bayan da rikicin Gabas ta Tsakiya ya janyo tashin farashin mai a watannin baya
- Raguwar farashin na zuwa ne yayin da ake samun alamun yiwuwar tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, duk da cewa har yanzu ba a cimma wata yarjejeniya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Farashin danyen mai ya ragu a kasuwannin duniya a ranar Laraba, bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa wakilan Amurka da Iran sun gudanar da tattaunawa “mai kyau” a Majalisar Dinkin Duniya.
A kasuwar Asiya da rana, farashin Brent, wanda shi ne ma’aunin danyen mai na duniya, ya koma dala 98.41 kan ganga, yayin da WTI ya sauka zuwa dala 89.23.

Source: Getty Images
Maganar da Trump ya yi
Yahoo News ta wallafa cewa Trump ya ce ganawar da jami’an kasashen biyu suka yi ta dauki tsawon sa’o’i uku, yana mai bayyana ta a matsayin mai kyau da kuma mai amfani.
Ya kuma ce ana shirin sake gudanar da wata ganawa tsakanin wakilan Amurka da Iran nan ba da dadewa ba.
Wannan bayani ya zo ne sa’o’i kadan bayan Trump ya gabatar da jawabi mai zafi a Majalisar Dinkin Duniya, inda ya ce yana fuskantar babban mataki tsakanin cimma yarjejeniya da Iran ko kuma lalata Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin gaggawa.
Rikicin ya shafi kasuwar mai
Kusan watanni bakwai bayan hare-haren Amurka da Isra’ila sun fara rikicin, Amurka da Iran sun shiga wani yanayi na rashin cimma matsaya.
A halin yanzu, Iran na ci gaba da rufe mashigar ruwan Hormuz, yayin da Amurka ke aiwatar da wani shingen teku kan tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
A Yemen ma, rikicin da ke tsakanin dakarun gwamnatin da Saudiyya ke mara wa baya da mayakan Houthi da Iran ke goyon baya ya shafi harkokin makamashi a yankin Bahar Maliya.
Stephen Innes na Quintex Intel ya ce ganawar Amurka da Iran na da muhimmanci saboda tana sauya yadda kasuwa ke kallon rikicin daga tsammanin kara tashin hankali zuwa yiwuwar tsarin diflomasiyya.

Source: Facebook
Raguwar farashin mai ta zo ne a daidai lokacin da rahotanni suka bayyana cewa Saudi Arabiya ta sake fara ayyukan bututun mai na Gabas zuwa Yamma.
An rage farashin fetur a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa matatar Dangote da sauran dillalan man fetur sun rage farashin fetur a manyan ma’ajiyoyi da ke Lagos, Fatakwal, Calabar da Warri.
Rahoton farashin ma’ajiyar man fetur ya nuna cewa wasu kamfanoni a Lagos sun rage farashin litar fetur da tsakanin N20 da N24.
Matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N1,350 zuwa N1,325, wato ragi na N25, yayin da Ascon, Integrated, Pinnacle da Sahara suka rage nasu da N24 zuwa tsakanin N1,326 da N1,327.
Asali: Legit.ng
