'Ba Shi da Lafiya,' Ayodele Ya Yi Hasashen Rasuwar Tinubu a kan Mulki

'Ba Shi da Lafiya,' Ayodele Ya Yi Hasashen Rasuwar Tinubu a kan Mulki

  • Fasto Elijah Ayodele, shugaban Cocin INRI, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu ba idan ya zarce
  • Ayodele ya ce idan hakan ta faru, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima na iya karɓar ragamar mulkin ƙasar kafin ƙarshen wa'adin
  • Faston ya danganta hasashensa da abin da ya ce yana gani game da lafiyar Tinubu, sai dai ba a tabbatar da ikirarin lafiyar shugaban ƙasar da kansa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Fasto Elijah Ayodele, shugaban Cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu ba idan ya sake lashe zaben shugaban ƙasa a 2027.

Ayodele ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa ranar Talata, inda ya ce wasu yanayi da ya danganta da lafiyar Tinubu na iya hana shi kammala wa'adin.

Kara karanta wannan

El Rufai ya aika sako ga 'yan uwa da abokan arziki bayan shafe fiye da kwanaki 200 a tsare

Shugaba Bola Tinubu da Primate Ayodele
Shugaban Najeriya a hagu, Primate Ayodele a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Primate Ayodele
Source: Facebook

Hasashen rasuwar Tinubu

A bidiyon da ya wallafa a X, Ayodele ya kwatanta hasashen nasa da abin da ya faru a zamanin tsohon Shugaba Umaru Musa Yar'Adua, wanda ya rasu yana kan mulki a shekarar 2010.

Ya ce irin wannan yanayi na iya faruwa idan Tinubu ya sake lashe zabe, wanda hakan zai iya kai ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya karɓi ragamar mulkin ƙasar.

“Idan Tinubu ya sake lashe zabe a karo na biyu, ba zai kammala wa'adin ba. Ina nan kan bakata, ba zai kammala ba. Abin da ya faru da Yar'Adua ko wani abu da zai hana shi kammalawa wanda zai kai ga kafa gwamnatin gaggawa, hakan na iya sa Shettima ya karɓe shi,”

In ji Ayodele.

Ya ƙara da cewa:

“Tinubu ba zai kammala wa'adinsa na biyu ba, in ji Ubangiji.”

Batun haduwa da Tinubu

Leadership ta wallafa cewa Fasto Ayodele ya kuma yi zargin cewa wasu mutanen da ke kewaye da Tinubu suna hana shi samun damar ganawa da shugaban ƙasar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gano abin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wahala bayan cire tallafin fetur

Ya ce mutanen ba sa son Tinubu ya saurari abin da ya bayyana a matsayin gaskiya, ciki har da shawarwarin da wasu malaman addini ke son isar masa.

“Mutanen da ke kewaye da Tinubu ba sa son ya ji gaskiya. Ba sa son ya saurari mutane irina,”

in ji shi.

Magana kan lafiyar Tinubu

Faston ya kuma yi kira ga iyalan Tinubu da su ƙara yin addu'a ga shugaban ƙasar, yana ikirarin cewa lafiyarsa ba ta da kyau.

Ya ce:

“Ba ku ganin abin da nake gani. Tinubu ba shi da lafiya sosai. Yana bukatar addu'a. Mata da 'ya'yan Tinubu, ku farka. Seyi! Ka taimaki Tinubu. Kada ka bari mahaifinka ya mutu.”
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sai dai ikirarin da Ayodele ya yi game da lafiyar shugaban ƙasa ba a tabbatar da su daga wata majiya mai zaman kanta ba, kuma hasashensa ba a ɗauke shi a matsayin rahoton likita ba.

Ga bayanin da ya yi a kasa:

Ana neman kayar da Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata ƙungiya mai suna Tinubu Must Go (TMG) ta rubuta wa wasu fitattun 'yan takarar adawa guda huɗu wasika, tana neman su haɗa kai.

Kara karanta wannan

Za su sha mamaki"; Malamin addini ya hango abin da zai iya fariwa da Tinubu a 2027

Ƙungiyar ta aika wasiƙun ne ga Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi na NDC, Omoyele Sowore na AAC da Gwamna Seyi Makinde na APM.

TMG ta ce ta ɗauki matakin ne bisa abin da ta bayyana a matsayin matsalolin tsaro, hauhawar farashi, talauci da rashin aikin yi domin kuma kawar da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng