Pantami da Dan Takarar APC Sun Shirya Kece Raini a wajen Muhawara a Gombe

Pantami da Dan Takarar APC Sun Shirya Kece Raini a wajen Muhawara a Gombe

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar APC, Dr Jamil Isyaku Gwamna, ya ce a shirye yake ya yi muhawara da sauran 'yan takara kan makomar jihar
  • Ɗan takarar gwamnan jihar na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, shi ma ya ce a shirye yake ya halarci muhawarar domin tattauna tsare-tsare, nasarori da makomar Gombe
  • Pantami ya ce yana shirye ya halarci muhawarar tun daga ranar Alhamis 24 ga Satumba 2026 da ƙarfe 10 na safe, yayin da Jamilu ya ce a shirye yake a kowace rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – 'Yan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyun APC da PDP, Dr Jamil Isyaku Gwamna da Farfesa Isa Ali Pantami, sun bayyana shirinsu na shiga muhawara kan yadda za a tafiyar da jihar idan aka zabe su a 2027.

Kara karanta wannan

Kaico: An kashe budurwa a gidan saurayinta kan rikicin daukar cutar ƙanjamau, HIV

Hakan na zuwa ne yayin da aka fara kamfen a hukumance kuma kowane dan takara ke cigaba da bayyana manufofinsa.

Jamilu Gwamna da Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a hagu da Jamilu Gwamna a dama. Hoto: Ibrahim Sani Shawai|Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Mai magana da yawun Gwamna, Ibrahim Sani Shawai, ya wallafa a Facebook cewa Jamilu a shirye yake ya fuskanci sauran masu neman kujerar gwamnan jihar domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban Gombe.

Jamilu ya ce a shirye yake

Shawai ya ce duk dan takarar da ke kiran a gudanar da muhawarar ya kamata ya shirya wurin da za a gudanar da ita, yana mai tabbatar da cewa Jamilu zai kasance a shirye “kowace rana, kowane lokaci”.

Ya ce muhawarar bai kamata ta tsaya kan maganganu, zarge-zarge da farfagandar siyasa kawai ba, sai dai a tattauna kan kwarewa, tarihi, alaka, damar jagoranci da sakamakon ayyukan da 'yan takarar suka taba yi.

“Jagoranci ya fi muhawara, yawan magana, zarge-zargen da ba su da tushe, karya da farfaganda. Siyasa da mulki ba gasar magana ce mara iyaka ba. Jagoranci ya shafi mutane, alaka, kwarewa, gogewa, cibiyoyi da sakamako,”

Kara karanta wannan

Da gaske ne mataimakin gwamna ya ce a yi wa Tinubu ruwan duwatsu?

In ji Shawai

Me Jamilu ke so a tattauna?

Mai magana da yawun dan takarar ya ce ya kamata muhawarar ta tabo batutuwan bunkasa dan Adam, samar da ayyukan yi, ilimi, kiwon lafiya, noma, ruwa, ababen more rayuwa, zuba jari da bunkasa masana'antu.

Ya kuma ce a tattauna kan karfafa matasa da mata, tare da duba ayyukan da Jamilu ya ce an samu a baya, ciki har da guraben ayyukan yi da tallafi ga 'yan kasuwa da kananan sana'o'i.

Pantami ma ya ce ya shirya

A nata bangaren, kungiyar Pantamiyya Movement ta bayyana cewa dan takarar gwamnan jihar na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya amince da kiran a gudanar da muhawara tsakanin 'yan takarar.

A cikin sanarwar da dan takarar ya wallafa a Facebook, an ce Pantami na son a bude muhawarar ga al'ummar Gombe tare da watsa ta ta kafafen yada labarai domin jama'a su saurara tare da tantance batutuwan da za a tattauna.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Sanarwar ta ce Pantami ya ce a shirye yake ya halarci muhawarar tun ranar Alhamis 24 ga Satumba 2026 da ƙarfe 10 na safe, idan sauran 'yan takarar ma suna a shirye.

Me Pantami ya ke so a tattauna?

Sanarwar ta ce Pantami na ganin ya kamata muhawarar ta mayar da hankali kan tsare-tsare, bayanan ayyuka, kwarewa da sakamakon da za a iya aunawa, ba batun mutane, zagi ko kalaman siyasa marasa tushe ba.

An kuma bayyana wasu ayyukan da kungiyar ta danganta da lokacin da Pantami ya rike mukamai a hukumomin gwamnatin tarayya, ciki har da jagorantar NITDA da kuma kasancewarsa Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani.

Sanarwar ta ce batutuwan da ya kamata a tattauna sun hada da samar da ayyukan yi, bunkasa ilimi da kiwon lafiya, noma, masana'antu, tattalin arziki da inganta dan Adam.

Sheikh Isa Ali Pantami
Dan takarar PDP a Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Pantami ya samu goyon baya

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar ’yan achaba a Jihar Gombe ta gudanar da wani taro a birnin Gombe domin bayyana goyon bayanta ga Farfesa Isa Ali Pantami.

An gudanar da taron ne a yammacin Talata, 22 ga Satumba 2026, a Pantamiyya Square, inda ’yan achaba daga sassa daban-daban na jihar suka hallara.

Shugabanni da wakilan kungiyar sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da wayar da kan sauran ’yan achaba da jama’a kan matsayinsu, tare da gudanar da ayyukansu cikin lumana da bin doka da oda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng