Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani da Suka Kai Hari Gidan Basarake dan Shekara 90

Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani da Suka Kai Hari Gidan Basarake dan Shekara 90

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake, Mallam Abubakar Lafiya mai shekaru 90 a duniya a jihar Neja
  • Rahotanni sun nuka cewa maharan sun yi awon gaba da magajin garin ne daga gidansa da ke Ka’ada bayan an yi harbe-harbe
  • Mazauna yankin sun bukaci jami’an tsaro su gaggauta daukarmataki domin kubutar da shi daga hannun miyagun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani magajin gari mai shekaru 90, Mallam Abubakar Lafiya, a kauyen Ka’ada da ke gundumar Dekara, karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar da ta agabatalokacin da ‘yan bindigar suka kutsa cikin gidan dattijon tare da yin harbe-harbe kafin su tafi da shi.

Neja.
Taswirar jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda aka sace basarake a jihar Neja

Kara karanta wannan

Ana shirin 2027, an gano bindigogi 399 da aka yi shirin kawowa Najeriya

Daily Trust ta rahoto cewa wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa wadanda suka kai harin sun mamaye gidan basaraken ne kafin su yi awon gaba da shi.

Ya ce Mallam Abubakar Lafiya ba dattijo ne kawai da ke rike da mukamin sarautar gargajiya ba, domin shi ne mahaifin hakimin gundumar Dekara na yanzu.

“Sace shi ya jefa mu cikin damuwa a Ka’ada, Dekara da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da mu, musamman saboda tsufansa. Magajin garin yanzu yana da shekaru 90,” in ji mazaunin.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali, yana mai cewa mazauna yankin na ci gaba da addu’ar Allah ya dawo da dattijon lafiya, cewar rahoton The Sun.

Mutane sun aika sako ga jami'an tsaro

Mazauna yankin sun yi kira ga jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa domin tabbatar da tsaron lafiyar Mallam Abubakar da kuma kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane.

Sun bayyana cewa tsufan wanda aka sace ya kara sanya lamarin zama abin damuwa, saboda bukatar kulawa ta musamman da mutum mai shekaru 90 ke da ita.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Mutane sun yi zanga zanga, an tare babbar hanyar Niger

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja bai yi nasara ba.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya suna motsa jiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Lambar wayar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba ta samu ba a lokacin da aka tuntube shi, don haka ba a samu karin bayani kan matakan da jami’an tsaro ke dauka domin ceto dattijon ba.

Lamarin ya kara jawo hankalin jama’a kan matsalar sace-sacen mutane da ayyukan ‘yan bindiga da ke ci gaba da jefa wasu al’ummomin jihar Neja cikin fargaba.

Yan sanda sun ceto matafiya a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda sun ceto wasu daga cikin mutane 13 da aka yi garkuwa da su bayan harin 'yan bindiga a hanyar zuwa Kano.

Wasu ƴan bindiga da su ka yi kwanton bauna a hanyar sun tare wata mota ɗauke da fasinjoji akalla 20 kafin a yi gumurzu da su, a ceto matafiyan.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya yaba wa mazauna yankin da masu amfani da hanyar saboda ba da sahihan bayanan gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262