Abubuwa Sun Tabarbare: Gwamnatin Plateau Ta Sanya Dokar Hana Fita

Abubuwa Sun Tabarbare: Gwamnatin Plateau Ta Sanya Dokar Hana Fita

  • Gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos da Mangu
  • Matakin ya biyo bayan hare-hare da kashe-kashe da suka yi sanadin mutuwar sama da mutane 20, ciki har da mata da yara, cikin kwanaki biyu
  • Hukumomin tsaro sun samu umarnin tabbatar da bin dokar hana fita da kuma dakatar da amfani da babura a yankunan da abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Gwamnatin Jihar Plateau ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos da Mangu, sakamakon hare-hare da kashe-kashe da aka samu a yankunan.

Rahotanni sun ce cikin kwanaki biyu, sama da mutane 20, ciki har da mata da yara, sun rasa rayukansu a hare-haren da suka shafi Mangu, Barkin Ladi, Bokkos da Riyom. An kuma kona gidaje da dama yayin hare-haren.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Gwamnatin Plateau ta sanya dokar ta baci
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Dokar hana fita ta fara aiki nan take

Kwamishiniyar Yaɗa Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap, ce ta sanar da dokar hana fita, inda ta ce ta fara aiki nan take, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Ta ce daga yanzu za a takaita zirga-zirga daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a yankunan da abin ya shafa, har sai an ba da wata sanarwa.

Kwamishiniyar ta ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana tabarbarewar doka da oda.

Gwamnati ta ce matakin na kare rayuka ne

Ramnap ta ce gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a Barkin Ladi, Bokkos da Mangu domin tabbatar da zaman lafiyar jama’a da dakile sababbin barazanar tsaro a yankunan.

Ta ce dokar za ta fara aiki daga ranar Litinin, 21 ga Satumba 2026, inda aka kayyade lokacin hana zirga-zirga tsakanin ƙarfe 6:00 na yamma da 6:00 na safe har sai an ba da wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke malamin addini da ke satar yara

Kwamishiniyar ta ce gwamnatin da Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ke jagoranta ta ɗauki matakin ne domin bai wa jami’an tsaro damar daidaita al’amura a yankunan, kare rayuka da kuma hana rugujewar doka da oda.

An umarci jama'a su bi dokar

Gwamnatin ta buƙaci mazauna ƙananan hukumomin da abin ya shafa su bi umarnin hana fita domin kare lafiyarsu da rayukansu, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

An kuma shawarci jama’a da su tsara harkokin kasuwanci, noma da sauran ayyukansu na yau da kullum bisa la’akari da lokacin da aka kayyade domin guje wa matsaloli ko saɓani a lokacin dokar.

An dakatar da amfani da babura

Ramnap ta ce an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da cikakken bin dokar hana fita tare da dakatar da amfani da babura a dukkan yankunan da abin ya shafa. Ta ce matakin ya fara aiki nan take.

Kwamishiniyar ta kuma tabbatar wa ’yan ƙasa masu bin doka cewa jami’an tsaro za su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa yayin da suke tabbatar da tsaro a yankunan.

An sanya dokar hana fita a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe fasinjoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki wata motar haya dauke da fasinjoji a Plateau.

Akalla fasinjoji tara aka kashe bayan 'yan bindiga sun budewa motarsu wuta a mahadar tituna ta Dungus Junction da ke ƙauyen Kuru, ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng