El Rufai Ya Aika Sako ga 'Yan Uwa da Abokan Arziki bayan Shafe Fiye da Kwanaki 200 a Tsare
- Nasir El-Rufai ya ce ba ya jin haushin tsofaffin abokai da abokan hulɗarsa da suka zaɓi yin shiru kan halin da yake ciki
- Ya ce goyon bayan da ya bai wa mutane da wasu manufofi a baya ya samo asali ne daga imaninsa da tarbiyya irin ta Arewa
- Kalaman tsohon gwamnan na jihar Kaduna na zuwa ne bayan ya shafe fiye da kwanaki 200 a tsare a hannun jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana kan shiru da wasu daga cikin tsofafin abokansa, abokan aikinsa da abokan hulɗarsa suka yi a lokacin da yake fuskantar matsaloli.
El-Rufai ya bayyana cewa bai kullaci wadanda suka zabi kin cewa komai kan halin da yake ciki ba.

Source: Facebook
El-Rufai ya bayyana matsayarsa ne a wata sanarwa mai taken “My Relationships and the Aftermath”, wadda ya sanya a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 23 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: EFCC ya ayyana sake neman Abdulrashid Maina ruwa a jallo, ta fadi dalili
Ya ce wasu mutane sun nuna damuwa kan yadda waɗanda ya taɓa tallafa wa a fili suka yi shiru kan halin da yake ciki.
‘Ban taimaki mutane domin su rama mini ba’
Tsohon gwamnan ya ce a tsawon rayuwarsa, goyon bayan mutane da kuma kare abubuwan da ya yi imani da su ya samo asali ne daga addininsa na Musulunci, tarbiyya irin ta Arewa, ƙa’idodinsa da kuma gamsuwa da abin da yake yi.
Ya ce bai taɓa yin hakan ne domin samun yabo, godiya ko tsammanin mutane su mayar masa da biki ba, sai dai saboda ya yi imanin cewa abin da ya yi shi ne daidai.
“Tsawon shekaru, na goyi bayan mutane kuma na kare abubuwan da na yi imani da su, wani lokaci cikin mawuyacin hali da kuma abin da shafe ni da kaina,” in ji shi.
Ya ce kowa na da ’yancin zaɓinsa
El-Rufai ya ce mutanen da ya taɓa tallafa wa a baya su ma suna da ’yancin yin nasu zaɓin a yanzu da yanayinsu ya sauya.
Ya ce wasu daga cikinsu na iya fitowa su nuna goyon baya gare shi, yayin da wasu za su iya yin shiru ko ma su nisanta kansu daga alaƙar da suka taɓa yi da shi.
“Dalilansu na su ne, kuma ba na son yin hukunci a kansu kawai saboda martaninsu ya bambanta da abin da wasu ko ma ni kaina zan yi tsammani,” in ji shi.
‘Ƙalubale kan bayyana ainihin alaƙa’
Tsohon gwamnan ya ce yanayi mai wahala na iya bayyana ainihin yanayin alaƙar da ke tsakanin mutane.
Ya ce abubuwan da ya koya cikin watannin da suka gabata na iya sa ya sake duba wasu daga cikin alaƙar da yake da su, amma ba tare da fushi ko nadama ba.
“Ƙalubale na da hanyar bayyana ainihin alaƙa,” in ji El-Rufai.
Ya ƙara da cewa wannan sake duba alaƙa bai kamata a fahimce shi a matsayin yin Allah-wadai ko zargi ga wasu mutane ba.
El-Rufai ya ce ba ya neman ramuwar gayya
El-Rufai ya ce ba ya nadamar tallafa wa mutane ko wasu manufofi a lokacin da ya yi imanin cewa yin hakan shi ne abin da ya dace.

Kara karanta wannan
"Zan iya rantsewa," Tsohon gwamna ya ce bai taba ganin shugaba kai tsari kamar Tinubu ba
Game da duk wani abin da ya ɗauka a matsayin rashin adalci, rashin godiya ko cutarwa da aka yi masa, El-Rufai ya ce ba ya neman ɗaukar fansa.
“Allah Maɗaukakin Sarki ne zai yi cikakken hukunci, kuma na bar wannan hukuncin a gare Shi, a duniya da kuma Lahira,” in ji shi.

Source: Twitter
Mai kusanci da El-Rufai ya fice daga ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na Arewa maso Yamma, Mallam Ja’afaru Ibrahim Sani, ya yi murabus daga jam’iyyar.
Jafaru Sani, wanda ya taɓa neman takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2027 ya rike kwamishina a gwamnatin Nasir El-Rufai.
Asali: Legit.ng
