Ana Jimamin Abin da Ya Faru a Neja, Ramin Hakar Ma'adanai Ya Rufta kan Mutane
- Mutane huɗu sun mutu bayan wani ramin hakar ma'adanai ya rufta a yankin Baban Rafi da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta Jihar Plateau
- Shugaban matasan Bokkos ya ce waɗanda abin ya rutsa da su sun haɗa da maza biyu da mata biyu, kuma danginsu sun binne su
- Rundunar ’yan sandan Plateau ta ce ba ta samu rahoto a hukumance kan lamarin ba, tana mai cewa masu hakar ma’adanai kan kasa kai rahoton irin waɗannan abubuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Bokkos, Plateau: Mutane huɗu, maza biyu da mata biyu, sun mutu bayan wani ramin hakar ma’adinai ya ruguje a yankin Baban Rafi da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta Jihar Plateau.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026, lokacin da waɗanda abin ya rutsa da su suke cikin ramin suna aikin haƙar ma'adanai.

Kara karanta wannan
An ga tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe mataimakin kwamandan rundunar tsaro a Plateau

Source: Original
Shugaban matasan Bokkos ya tabbatar da lamarin
Shugaban matasan Bokkos, Daniel Tula, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da Channels Tv.
Tula ya ce mutane huɗun sun makale ne bayan ramin ya ruguje, inda daga bisani danginsu suka binne gawarwakinsu.
Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan hatsari a yankin, lamarin da ya janyo ƙarin damuwa kan lafiyar masu aikin hakar ma’adanai a yankin.
A cewarsa, har yanzu ana ƙoƙarin gano cikakken abin da ya haddasa rushewar ramin, amma ya tabbatar da cewa waɗanda suka mutu suna aikin haƙar tin ne a lokacin da ramin ya ruguje.
’Yan sanda ba su samu rahoto ba
Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Plateau ta ce ba ta samu wani rahoton hukumance game da mutuwar mutanen huɗun ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Alfred Alabo, ya bayyana cewa har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba.
Alabo ya ce masu hakar ma’adinai kan yi kasa a gwiw wajen kai rahoton irin waɗannan hatsarori ga ’yan sanda, lamarin da ke sa rundunar samun wahalar tantance abin da ya faru cikin gaggawa.
Sai dai ya yi alkawarin cewa zai bayar da ƙarin bayani da zarar ya samu cikakken rahoto daga jami’an da ke yankin.
Ba a samu shugaban ƙaramar hukumar ba
An kuma yi ƙoƙarin samun shugaban ƙaramar hukumar Bokkos domin tabbatar da lamarin, amma bai amsa kiran waya da aka yi masa ba.
Mutuwar waɗannan masu hakar ma’adanai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matakan tsaro da haɗurran da ke tattare da ayyukan hakar ma’adinai a wasu al’ummomin Jihar Plateau.

Source: Facebook
Bago ya tabbatar da mutuwar mutane a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya tabbatar da mutuwar mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba yayin da suke tsare a hannun hukumar NSCDC a Minna.
Gwamna Bago Bago ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamitin bincike domin gano abubuwan da suka faru da kuma dalilin da ya jawo mutuwar mutanen
Asali: Legit.ng
