Farfesa Safiyanu Ishiaku Ya Kare Musulunci daga Jingina Masa Ta'addanci

Farfesa Safiyanu Ishiaku Ya Kare Musulunci daga Jingina Masa Ta'addanci

  • Farfesa a jami'ar jihar Gombe, Safiyanu Ishiaku, ya gabatar da lakca ta 26 ta jami'ar kan zaman lafiya tsakanin addinai a Najeriya
  • Ya ce mafi yawan rikice-rikicen da ake kira na addini a Najeriya suna samo asali ne daga siyasa da bambancin ƙabila, ba addini ba
  • A na shi nangaren, shugaban jami'ar ya danganta taken lakcar da muhimmancin zaman lafiya yayin da Najeriya ke tunkarar zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Farfesa a tsangayar koyar da addinin Musulunci a Jami'ar Jihar Gombe (GSU), Safiyanu Ishiaku, ya bayyana cewa Musulunci bai yarda da tilasta wa mutane karɓar addini ko kashe waɗanda ba Musulmi ba.

Farfesan ya bayyana haka ne ranar Talata yayin da yake gabatar da lakca ta 26 ta jami'ar game da alakar Musulmi da wadanda ba Musulmi ba.

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

Farfesa Safiyanu Ishiaku
Lakacin da Farfesa Safiyanu Ishiaku ke gabatar da lakca. Hoto: Gombe State University, Gombe Nigeria
Source: Facebook

A sakon da jami'ar ta wallafa a Facebook, Farfesan ya yi Allah wadai da masu aikata ta'addanci da sunan addini, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka sun saɓa wa koyarwar Musulunci.

Ta'addanci ya saɓa wa Musulunci

A cewar Farfesan, masu tilasta wa mutane karɓar Musulunci ko kashe waɗanda ba Musulmi ba suna aikata abin da ya saɓa da ainihin koyarwar addinin.

Ya ce:

"Ta'addancin da muke gani a yau, inda ake tilasta wa mutane karɓar Musulunci ko kuma kashe waɗanda ba Musulmi ba da sunan addini, ba koyarwar Musulunci ba ce ko kaɗan.
"Kuskure ne da rashin fahimta. Musulunci ba ya tilasta wa kowa ya karɓe shi."

Ya kuma buƙaci masu son fahimtar Musulunci su koma ga Alƙur'ani da ingantattun hadisai na Annabi Muhammadu (SAW), maimakon su yanke hukunci da halayen wasu Musulmi.

Rikice-rikice da ake a Najeriya

Farfesa Ishiaku ya kuma bayyana cewa mafi yawan rikice-rikicen da ake kira na addini a Najeriya ba addini ne ke haddasa su ba.

Kara karanta wannan

'Fulani ba 'yan ta'adda ba ne,' Sarkin Musulmi ya yi magana kan matsalar tsaro

Ya ce galibinsu suna da alaƙa da siyasa, bambancin ƙabila ko matsalolin tattalin arziki, amma ana ba su siffar rikicin addini saboda tasirin addini a cikin al'umma.

Farfesa Safiyanu Ishiaku a GSU
Lokacin da ake karrama Farfesa Safiyanu Ishiaku a GSU. Hoto: Gombe State University, Gombe Nigeria
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa kaɗan ne daga cikin rikice-rikicen da suka taɓa faruwa a tarihin Najeriya da suka samo asali kai tsaye daga addini, yayin da sauran aka yi amfani da addini ne domin cimma wasu manufofi.

Ya kuma gargadi Musulmi kan bin mutane ido rufe, yana mai cewa fifita biyayya ga mutane fiye da koyarwar Musulunci ya jawo ɓata sunan addinin.

Magana kan almajirai

A wani labarin, mun ruwaito cewa uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta buƙaci ƙasar Saudiyya ta haɗa kai da Najeriya wajen inganta ilimin Almajirai da yara marasa zuwa makaranta.

Ta bayyana cewa rashin bai wa waɗannan yara ilimi na zamani da na addinin Musulunci tare na iya ƙara barazana ga tsaron ƙasar.

Oluremi Tinubu ta ce haɗa ilimin Alƙur'ani da ilimin boko zai taimaka wajen samar wa Almajirai makoma mai kyau da rage matsalolin rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng