Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da ɗalibansa mata

Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da ɗalibansa mata

  • Jami'ar jihar Kwara (KWASU) ta sallami wani malami, Pelumi Adewale, bisa zargin da ake masa na neman ɗalibai da lalata
  • Rahotanni sun bayyana cewa lakcaran ya yi wa wata ɗaliba barazanar kada ita a kwas ɗin da yake ɗauka idan bata amince masa ba
  • A halin yanzun lamarin na gaban kotu, inda alkali ya ɗage sauraron shari'an zuwa 8 ga watan Disamba

Kwara - Jami'ar jihar Kwara dake Malete, ta sallami ɗaya daga cikin malamanta, Pelumi Adewale, bisa zargin yunkurin lalata da ɗalibarsa, Tosin Adegunsoye.

Mataimakin shugaban KWASU, Mustapha Akanbi, shine ya bayyana haka a Ilorin ranar Litinin, yayin da yake fira da manema labarai kan bikin yaye ɗalibai karo na 8 da 9.

Akanbi yace tsohon malamin ya yi amfani da kasancewarsa ɗaya daga cikin lakcarorin jami'ar KWASU wajen ɓata mata suna a idon mutane, kamar yadda Punch ta ruwsito.

Kara karanta wannan

Najeriya ba ta samu ko sisi ba daga ɗanyen man fetur a watan Satumba, inji NNPC

Kwasu
Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da ɗalibansa mata Hoto: punchng.com
Asali: UGC

VC yace:

"A halin yanzu lamarin na hannun jami'an tsaro kuma tuni an shigar da ƙara gaban kotu, amma ina son sanar daku cewa mutumin ya zama tsohon malamin KWASU."
"Ya zama tamkar cin mutunci ne ga jami'ar mu, kuma ba zamu iya cigaba da zama da masu irin wannan halayyan ba."

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa a ranar 11 ga watan Satumba, aka gurfanar da Adewale gaban kotun Majistire dake zamanta a Ilorin kan zargin lalata da ɗalibai.

Yadda aka damke lakcaran

A bayanan farko, Adegunsoye, ta bayyana cewa malamin da aka sa ya ɗauke su kwas ɗin MLS 212, ya mata barazanar kada ita a jarabawa matukar ba ta amince ya yi lalata da ita ba.

Bisa barazanar da ya mata, yan sanda sun umarci ɗalibar ta buga wasa da malamin domin a samu cikakkiyar shaida a kansa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jami'an DSS sun damke Janar Dambazau a jihar Kano

Malamin ya gayyaci ɗalibar har gidansa dake kan hanyar Taoheed da misalin ƙarfe 8:30 na dare, inda ya bata sabuwar jarabawa da takardar amsa jarabawa ta KWASU.

Malamin ya bata damar sake rubuta jarabawa amma da sharaɗin cewa zata amince su yi lalata har zuwa gari ya waye.

Yayin da ake cikin haka ne jami'an dake ɓoye suna sa ido kan abinda ke faruwa suka yi ram da malamin.

Ya zaman kotu ya kasance?

Yayin zaman kotun, mai shari'a Ibrahim Mohammed, ya baiwa wanda ake zargi beli a kan kudi naira dubu N200,000.

Daga nan kuma sai alkalin ya ɗage sauraron ƙarar sai zuwa ranar 8 ga watan Disamba, 2021.

A wani labarin na daban kuma kamfanin mai na NNPC yace Najeriya ba ta samu kudin shiga ba daga ɗanyen mai da take hako wa

A rahoton da kamfanin ya saka a shafin yanar gizo, NNPC ya bayyana cewa duk da hako ɗanyen mai sama da ganga miliyan daya a rana, babu wanda ya siya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Iyayen Ango da Yan uwansa sun mutu awanni kadan bayan kammala daura Aure

Shekaru da dama da suka shuɗe, kasashen Indiya, China, da kuma kasar Amurka, sune suka kasance masu siyan ɗanyen mai da Najeriya ke samarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel