Lalata da dalibai don maki: Wacce abun ya faru da ita ta gudanar da zanga-zanga a Kaduna

Lalata da dalibai don maki: Wacce abun ya faru da ita ta gudanar da zanga-zanga a Kaduna

Salamatu Bello, wacce ake zargin malamin jami’a da lalata da ita, ta gudanar da zanga-zanga a kewayen birnin Kaduna domin nuna halin wuyar da dalibai mata ke shiga a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa mata, dauke da kwalin sanarwa da rubutu kan cin zarafin mata, ta yi magana da manema labarai akan lamarin.

Bello ta ce an ci zarafinta ta hanyar lalata da ita a lokacin da take a matsayin daliba a jami’ar Ahmadu Bello, Zaria a 2010, sannan ta yi zargin cewa malamin da ya ci zarafinta a yanzu yana tare da jami’ar jihar Kaduna.

Koda dai ta ki bayar da cikakken sharhi akan abunda ya wakana, Bello tace za ta gurfana a gaban kwamitin da jami’ar jihar Kaduna ta kafa domi binciken malamin da ke da hannu a lamarin.

A cewarta cin mutuncin dalibaiu mata ya dade yyana wakana a makarantun jami’a, sannan kuma a koda yaushe wadanda abun ya shafa ba sa son fitowa fili su yi magana.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), a ranar Laraba ta dauki mataki kan daya daga cikin malamanta, Mista Bala Umar da aka fi sani da A.B. Umar kan zargin da ake masa na neman yin lalata da daliba don ya bata maki.

KU KARANTA KUMA: Wani dan bautar kasa ya yiwa wani yaro duka har lahira a Kano

A taron da muhukuntar Jami'ar suka yi a ranar Laraba, KASU ta ce an kafa kwamiti don bincike kan zargin da ake yi wa Umar bayan zanga-zangar da wata mata tayi.

Matar da ba a fadi sunan ta ba, ta yi ikirarin cewa cewa Umar bai cancanta ya zama malami a jami'ar ba domin an kore shi ne daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kan yin lalata da daliba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel