Jami'ar Ahmadu Bello
Nasa'i Muhammad Gwadabe ya rantse da Allah SWT cewa bai yi lalata da dalibarsa mai aure ba, ya karyata zargin da ake yi masa. Malamin jami'ar ya bada bangarensa.
Dattawan Katsina da kungiyoyi daban-daban na neman lallai jami'an tsaro su saki Dr. Bashir Kurfi bayan kama shi da zarginsa da yin kalaman bata sunan gwamnati.
Kamfanin Transact zai ba daliban jami'o'i 20 a Najeriya kyautar kudi bayan sun yi zarra a fadin duniya. Kowane dalibi zai samu kudi N100,000 kyauta.
Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary ya fadawa mabiya darika cewa duk hanyar da za su bi, su je su bi domin yin ibada. Ibrahim Maqary ya yi zargin ana danne darika a jami'a
A labarin nan, za a ji Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da yadda Najeriya za ta ci gajiyar fasahar AI da taimakon jami'o'in da ke kasar.
Wata mota ta zubar da tarin harsashi a kusa da kofar shiga jami'ar ABU Zariya. Ana zargin cewa motar za ta wuce Katsina ne kuma an mika harsashin ga jami'an tsaro.
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna ta karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ya zarge ta da kera makamin nukiliya.
An fitar da jerin jami'o'i mafi nagarta a Najeriya a 2026. Jami'ar Bayero da ke Kano ta zo ta uku yayin da jami'ar ABU ta zamo ta shida. Jami'ar Ibadan ce ta daya.
Gwamnatin tarayya ta ba kungiyar malaman jami'o'in kasar nan baki a kan shirinta na tsundauma yajin aiki, ta ce a ci gaba da zama, za a samu biyan bukata.
Jami'ar Ahmadu Bello
Samu kari