Jami'ar Maryam Abacha Ta Dauki Mataki bayan Bankado Badala a Wurin Kwanan Dalibai

Jami'ar Maryam Abacha Ta Dauki Mataki bayan Bankado Badala a Wurin Kwanan Dalibai

  • Jami’ar Maryam Abacha reshen jihar Kano ta rufe dakunan kwanan dalibai mata guda biyu nan take bisa zargin lalata da rashin bin doka
  • An rufe dakunan Al-Ansar da Indabo da ke Hotoro da titin UDB a Kano saboda ayyukan da ba su dace ba da gilmawar bakin fuska a dakunan
  • Jami’ar ta umarci daliban da abin ya shafa da su bar wuraren kwana bayan jarrabawar zangon nan, kuma ana aiki da jami'an tsaro kan batun

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar gudanarwar jami’ar Maryam Abacha (MAAUN) ta ba da umarnin gaggawa na rufe wasu dakunan kwanan daliban mata guda biyu saboda zargin rashin da’a.

Dakunan kwanan dai mallakin masu zaman kansu ne da jami’ar ta amince da su domin amfanin dalibai, ciki har da Al-Ansar da Indabo, wadanda ke kan titin Hotoro da UDB a cikin birnin Kano.

Maryam
Jami'ar Maryam Abacha ba da umarnin rufe dakunan kwanan dalibai 2 a Kano Hoto: Maryam Abacha American University of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sanarwar rufe wuraren ta fito ne daga mataimakin shugaban jami’ar kan al’amuran dalibai, Dr. Hamza Garba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rufe wurin kwanan daliban Maryam Abacha

Punch ta ruwaito cewa shugabannin jami’ar sun bayyana cewa wannan mataki wani bangare ne na kokarinsu na tabbatar da amintattun wuraren kwana ga dalibai mata.

Sannan ta jaddada cewa wannan yana daga cikin tabbatar da manufar jami’ar na rashin yarda da kowanne irin hali na lalata a cikin jami’a.

Jami'a
Jami'ar Maryam Abacha ta ce ba za ta zuba ido dalibai su lalace ba Hoto: Maryam Abacha American University of Nigeria
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

“An umarce ni da na sanar da iyaye da dalibai cewa jami’ar ta janye amincewarta da dakunan kwanan dalibai mata na Al-Ansar da Indabo da ke kan titin UDB da Hotoro."

Dalibai sun fusata jami’ar Maryam Abacha

Hukumar gudanarwar jami’ar ta ce ta lura da ayyuka da motsin da ba su dace ba a yankin dakunan, ciki har da raba wurin da wasu mutanen da ba a san su ba.

A cewar sanarwar:

“Kin bin ka’idoji ya jawo abubuwa marasa dadi daga ciki har da halayen da ba su dace ba, karancin ruwa da wutar lantarki, tayar da hankula daga dalibai, fitar dare ba tare da izini ba, da kuma raba wurin da baƙin fuska. Wadannan matsalolin suna barazana ga lafiya da zaman lafiya na dalibanmu.”
“Saboda haka, an umarci dukkanin daliban da abin ya shafa da su fice daga dakunan kwanan nan take bayan kammala jarabawa, kuma kada su sake komawa wurin don kare lafiyarsu da tsaronsu. A halin yanzu kuma, jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cikakken bin wannan doka.”

Jami’ar ta kuma ja kunnen dalibai da iyayensu cewa ba za ta dauki alhakin duk wani abin da zai faru sakamakon kin bin wannan umarni ba.

Gwamnati za ta taimaki daliban Kano

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta amince da kashe sama da N3bn domin daukar nauyin jarrabawar dalibai 141,175 da suka ci jarrabawar tantancewa ta shekarar 2024.

A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya fitar, ya ce za a yi amfani da kudin don biyan kudin NECO, NABTEB da NBAIS.

Sanarwar ta jaddada cewa duk daliban da suka ci wannan jarrabawa sun cancanci zauna jarabawar kammala sakandare na bana, ciki har da daliban da ke karatun Larabci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.