Murkushe Ƴan Adawa da abu 3 da Ƴan Najeriya Ke Fargaba game da Ƴansandan Jihohi
Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin kafa rundunar 'yansandan jihohi, bayan Majalisar Wakilai ta riga ta amince da shi a baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kudirin, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar domin a yi wa kundin tsarin mulki gyara, zai koma gaban majalisun dokokin jihohi domin su amince da shi kafin shugaban ƙasa ya rattaba hannu.

Source: Twitter
Fargaba game da kafa ƴansandan jihohi
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kafa rundunar 'yansandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Sai dai duk da haka, masana da wasu masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa kan yiwuwar matsalolin da tsarin zai iya haifarwa idan ba a shimfiɗa masa ingantattun dokoki ba.
1. Fargabar murkushe 'yan adawa
Daya daga cikin manyan damuwar masu suka shi ne yiwuwar gwamnonin jihohi su yi amfani da 'yansandan jihohin wajen cimma muradun siyasa.
Masanin harkokin tsaro, Dr. Audu Bulama Bukarti, ya ce akwai fargabar gwamnoni su rika amfani da rundunar wajen takura wa masu adawa da su.
A cewarsa, yadda ake zargin wasu gwamnoni da yin tasiri kan wasu hukumomin jihohi ya nuna akwai bukatar sanya tsauraran matakan kariya domin kauce wa cin zarafin iko.
Ko da yake kudirin ya tanadi cewa kwamishinan 'yansandan jiha na iya ƙin bin umarnin gwamna idan ya saba wa doka, masu suka na ganin hakan kadai ba zai wadatar ba.
2. Matsalar bambancin ƙabila da addini
Wasu masana sun ce Najeriya har yanzu na fama da matsalolin da suka shafi bambancin ƙabila da addini.
Bukarti ya yi gargadin cewa a wasu jihohi akwai yiwuwar a yi amfani da rundunar wajen nuna wariya ga wasu al'ummomi, musamman idan shugabanni ba su yi adalci ba.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi
Ya ce hakan na iya ƙara dagula zaman lafiya a yankunan da tuni ke fama da rikice-rikice.
3. Tambaya kan ƙarfin tattalin arziƙin jihohi
Gudanar da rundunar 'yansanda na bukatar kuɗaɗe masu yawa domin biyan albashi, samar da kayan aiki, motocin sintiri, makamai da gina ofisoshi.
Masu nazari sun yi tambaya ko dukkan jihohin Najeriya za su iya ɗaukar wannan nauyi na tafiyar da 'yansandan jihohin ba.
Shugaban gamayyar ƙungiyar al'ummar Arewa (CNG), Jamilu Aliyu Charanchi, ya ce idan har rundunar 'yansandan Najeriya na fama da ƙarancin kayan aiki da walwala, akwai buƙatar a yi nazari sosai kafin a ƙara wata runduna.
Ya yi gargadin cewa rashin isassun kuɗi na iya janyo cin hanci da rashawa a cikin rundunar.
4. Rikicin hurumin aiki tsakanin jihohi
Wani batu da ake ta tattaunawa shi ne yiwuwar samun rikici tsakanin 'yansandan jihohi da na tarayya.
Bukarti ya bayyana cewa saboda wasu iyakokin jihohi ba su da cikakkiyar fayyacewa, hakan na iya haddasa rudani game da hurumin gudanar da aiki.
Haka kuma ya ce idan ba a fayyace aikin kowace runduna ba, ana iya samun cin karo tsakanin jami'an tsaro a yayin gudanar da aiki.
Abin da gwamnoni ke cewa
A daya bangaren kuma, gwamnoni sun dage cewa kafa 'yansandan jihohi shi ne mafita ga matsalar tsaro, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce Najeriya na da mutane sama da miliyan 230, amma adadin jami'an 'yansanda bai kai yadda ake bukata ba.

Source: Twitter
Ya ce akwai wuraren da mutum zai yi tafiya mai nisa ba tare da ganin jami'an tsaro ba, lamarin da ke nuna bukatar ƙarin jami'an tsaro.
A cewarsa, jami'an da aka dauka daga cikin al'ummar yankin sun fi sanin hanyoyi, dazuka da kuma mutanen da ke zaune a yankinsu, wanda hakan zai taimaka wajen yaƙi da miyagun laifuka.
Sai dai ya bayyana cewa a halin yanzu kundin tsarin mulkin Najeriya bai bai wa jihohi damar kafa ofisoshin 'yansanda ba sai da amincewar shugaban rundunar 'yansandan ƙasa.
Martanin Buba Galadima kan 'yansandan jihohi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jigon NDC, Buba Galadima, ya yi magana game da shirin kafa yan sandan jihohi wanda ake ta ce-ce-ku-ce a kai.
Buba Galadima ya gargaɗi cewa kafa 'yan sandan jihohi na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya da haɗin kan Najeriya.
Ya yi nuni da yadda aka yi amfani da 'Native Authority Police' a baya wajen danniya, yana gargadin cewa irin wannan na iya maimaituwa.
Asali: Legit.ng


