Ambaliya Ta Mamaye Yankunan Legas, Hanyoyi Sun Yi Makil, Lantarki Ta Katse

Ambaliya Ta Mamaye Yankunan Legas, Hanyoyi Sun Yi Makil, Lantarki Ta Katse

  • Rahoto ya nuna cewa mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a yankuna da dama na jihar Legas, inda ya mamaye unguwanni
  • Ambaliyar ta lalata wasu muhimman abubuwan da suka shafi wutar lantarki, lamarin da ya jawo katsewar wuta da takaita zirga-zirga
  • Yayin da ake cikin damuwa, mazauna yankunan sun alakanta matsalar da toshewar magudanan ruwa da jihar ke fama da shi a yanzu haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Ambaliya ta mamaye al'ummomi da dama a jihar Legas a ranar Talata bayan shafe sa'o'i ana ruwan sama mai ƙarfi.

Ruwa ya mamaye gidaje da tituna, ya hana zirga-zirga tare da katse wutar lantarki a wasu sassan jihar bayan lalacewar wasu muhimman kayayyaki.

Ambaliyar ruwa a Legas
Yadda wata mota ta shiga ruwa a Legas yayin da ake ambaliya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewaa ruwa ya cika yankunan FESTAC, Gbagada, Evans, Olushi, Anikantamo da Adeniji Adele a Legas, inda mazauna ke ratsawa cikin ruwa.

Kara karanta wannan

Iyayen daliban da aka sace sun rusa kuka bayan ziyarar tawagar Zulum

Ambaliya ta mamaye gidaje a Legas

Manema labarai da suka bibiyi lamarin a Ikeja sun lura cewa ambaliyar ta shiga gidaje da shaguna da dama, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna ƙaura na ɗan lokaci saboda tsoron ƙarin muni.

Ambaliyar, wadda toshewar magudanan ruwa da robobi da kuma rashin isassun hanyoyin wucewar ruwa suka ƙara muni, ta sa tituna da dama suka cika da ruwa har zuwa gwiwa.

Wani mazaunin Ikeja, Abidemi Raji, ya ɗaura alhakin ambaliyar kan rashin kyakkyawan tsarin gina tituna da kuma toshewar magudanan ruwa.

Ya ce:

“Yadda aka gina titin na taimakawa wajen haddasa ambaliya. Duk da akwai magudanar ruwa, sai bayan minti 30 zuwa awa ɗaya da tsayawar ruwan sama ne ruwa ke fara raguwa saboda yawansa.”

Ruwa ya mamaye tituna

Ruwan saman ya kuma mamaye tituna da dama a yankin Festac da ke Ƙaramar Hukumar Amuwo-Odofin, inda ya kawo cikas ga zirga-zirga tare da jefa mazauna da matafiya cikin matsala.

Kara karanta wannan

Kano: An gano abin da ya jawo mummunan arangama tsakanin manoma da makiyaya

Wani bidiyo ya nuna yadda manyan tituna da hanyoyin cikin unguwanni suka cika da ruwa, inda masu tafiya a ƙafa suka ratsa cikin ruwa, yayin da direbobi ke fama da wahalar wucewa.

Wata mazauniyar yankin, Okeke Mmesoma, ta bayyana cewa ambaliyar ta zama matsala da ake fuskanta akai-akai.

Ta ce:

“Duk lokacin da aka yi ruwan sama mai ƙarfi wannan wuri yana cika da ruwa. Bayan ruwan ya tsaya ne kawai ruwa ke fara raguwa. Takalma na sun jike da safiyar yau lokacin da nake zuwa aiki.”
Ambaliya a jihar Legas
Motoci sun nutse yayin ambaliya a Legas. Hoto: Iyida Faith Chinenye
Source: Facebook

An kuma samu rahoton ambaliya a Ajah, yayin da titunan Adeniji Adele, Evans, Olushi da Anikantamo da ke tsibirin Legas suka cika da ruwa.

Ga wasu bidiyon yadda ruwa ya mamaye wurare da Vanguard ta wallafa a X:

Lantarki ta katse a Legas

Ruwan saman ya kuma haddasa katsewar wutar lantarki bayan da ambaliya ta lalata kayan aiki a tashar rarraba wuta ta Oworo mai ƙarfin 132/33kV.

Kamfanin rarraba wuta na jihar ya ce yana aiki tare da TCN domin dawo da wutar lantarki da zarar an gyara kayan aikin da suka lalace.

NiMet ta yi hasashen ruwa

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya aika sakon gaggawa ga gwamnati kan daliban da aka sace a Borno

A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta sanar da wasu jihohin da za a yi ruwan sama a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa jihohin Kano, Gombe, Taraba, Legas, Ondo, Rivers da sauransu za su samu ruwa bisa hasashen da hukumar ta yi.

NiMet ta bukaci mutane su dauki matakan kariya da ta fada domin jama'a su kaucewa fadawa cikin hadari a lokacin da ruwan sama ya barke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng