
Abuja







Yayin da ake ta korafi kan ƙirƙirar sababbin jihohi, Cibiyar Kare (CHRICED) ta zargi APC da amfani da lamarin don yaudarar 'yan Najeriya kan zaben 2027.

Tsohon shugaban inshora ta NHIS ya ce hukumar EFCC sun kama shi kamar sun kama Bello Turji. Ya fadi yadda ya zauna a wajen EFCC da zama a kurkukun Kuje.

Majalisar Wakilan Tarayya ta karrama marigayi tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Murtala Muhammed, ta ce za ta rika tunawa da shi a kowace shekara.

Farfesa Usman Yusuf ya fito da bayanai kan maganganun da ya yi a taron matasan Arewa a jihar Bauchi ana daf da kama shi, ya soki Faransa da Bola Tinubu.

Bayan Kungiyar NBMOA ta maka Arewa24 a gaban kotu bisa zargin gudanar da ayyuka ba tare da lasisi ba a Najeriya za a saurari shari’ar a birnin Abuja.

An samu matsala a tushen wuta naƙasa, wanda ya janyo daukewar wuta a yankunan Abuja, Kogi, Neja da Nasarawa. Ana kan aikin gyara tare da hukumomi.

Yayin da ake tuhumar tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta NHIS, Babbar kotun Abuja ta ki amincewa da ba da belin Farfesa Usman Yusuf kan badakalar kudi.

A makon da ya gaba majalisar wakilai ta karanta wasu bukatu da aka gabatar a gabanta na kirkirar sababbin jihohi 31 bayan 36 da ake da su a Najeriya.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karbi shugabannin NNPP da suka koma APC saboda rashin tabbas da manufofin Kwankwasiyya marasa amfani.
Abuja
Samu kari