Muhimman Abubuwa 10 game da Dokar 'Yan Sandan Jihohi ta Najeriya

Muhimman Abubuwa 10 game da Dokar 'Yan Sandan Jihohi ta Najeriya

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta zartar da dokar kafa ‘yan sandan jihohi bayan matsin lamba mai ƙarfi daga gwamnoni da kuma ƙaruwar matsalolin tsaro a ƙasar
  • Dokar ta sauya tsarin jami’an tsaron ƙasar ta hanyar maye gurbin sunan 'yan sanda domin samar da tsarin aiki da ya fi karkata ga fararen hula
  • An samar da tsarin kuɗi guda biyu da kuma matakan gudanarwa domin tabbatar da ‘yancin gashin kai ta fuskar kuɗi da hana amfani da ‘yan sanda a harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta zartar da dokar kafa ‘yan sandan jihohi bayan ƙaruwar matsalolin tsaro a faɗin ƙasar da kuma ci gaba da matsin lamba daga gwamnoni.

Sabon tsarin doka ya sauya tsarin tsaro ta hanyar mayar da aikin tabbatar da doka daga kasancewa ƙarƙashin gwamnatin tarayya kaɗai zuwa nauyin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kawo hanyar magance rikicin manoma da makiyaya

'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya na fareti a Abuja. Hoto: Nigeria Police
Source: Facebook

Bisa ga takardun hadimin Bola Tinubu, Dada Olusegun ya wallafa a X, dokar ta ƙunshi sauye-sauye masu yawa na gudanarwa da aka tsara domin sabunta tsarin aikin ‘yan sanda.

Abubuwa 10 kan 'yan sandan jihohi

Ga muhimman abubuwa 10 a dokar ‘an sandan jihohi ta Najeriya ta 2026 da majalisar wakilai da ta dattawa suka amince a kafa:

1. Sauya sunan 'yan sanda

Dokar ta maye gurbin kalmomin “Force” da “Service” a dukkan nassosin dokar 'yan sanda, inda aka sake sanya wa rundunar sunan da ya ƙunshi kalmar 'Service'.

Wannan sauyi na da nufin mayar da jami'an daga tsarin soja mai aiki bisa umarni zuwa hukuma mai aiki a saukake kan hulɗa da al’umma.

2. Cin gashin kan jihohi

Kowace jiha a tarayyar Najeriya tare da Babban Birnin Tarayya (FCT) za ta samu ikon kafawa da tafiyar da nata tsarin ‘yan sanda mai zaman kansa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: PRP ta kawo cikas a shirin ƙirƙiro rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya

Legit ta rahoto cewa waɗannan sababbin hukumomi za su yi aiki tare da rundunar tarayya maimakon yin gogayya da ita.

3. Sake tsarin majalisar ‘yan sanda

Majalisar ‘yan sanda ta Najeriya za ta samu sabon kundin tsarin mulki domin duba manufofin ƙasa da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci.

Kwamitin gudanarwarta zai ƙunshi shugaban kasa a matsayin shugaba, gwamnoni, shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda da kuma sufeto janar na ‘yan sanda.

4. Kafa majalisun ‘yan sanda

Domin tabbatar da sa ido a matakin jiha ba tare da katsalandan daga gwamnatin tarayya ba, kowace jiha za ta kafa majalisar ‘yan sandan jiha.

TVC ta rahoto cewa gwamnan jiha ne zai jagorance ta, yayin da Kwamishinan ‘yan sanda na jiha zai kasance sakataren majalisar.

5. Tsarin kuɗi guda 2

Dokar ta samar da tsarin kuɗi daban-daban domin tabbatar da ayyukan ‘yan sanda sun kubuta daga matsin lambar rashin kuɗi.

Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ɗaukar nauyin rundunar tarayya ta hanyar asusun kudin shiga bai daya, yayin da gwamnatocin jihohi za su ɗauki cikakken nauyin kuɗin rundunoninsu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi maganar da ta ba da mamaki kan tsaro

6. Tsayayyen wa’adin jagoranci

Sufeto Janar na ‘yan sanda a matakin tarayya da kwamishinonin ‘yan sandan jihohi za su yi wa’adi guda ɗaya na shekara huɗu ba tare da damar sabuntawa ba.

Gwamnoni ne za su naɗa kwamishinonin ‘yan sandan jihohi bisa shawarar majalisar ‘yan sandan jiha, sannan majalisar dokokin jiha za ta tabbatar da naɗin.

Jami'an 'yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya a wajen taron zaman lafiya na majalisar dinkin duniya. Hoto: Nigeria Police
Source: Facebook

7. Sake tsarin hukumar ‘yan sanda

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta yanzu za ta takaita aikinta ga kula da jami’an rundunar tarayya da ke karkashin shugaban kasa ne kaɗai.

Saboda haka, jihohi za su kafa nasu hukumar kula da ayyukan ‘tan sandan jiha domin kula da ɗaukar ma’aikata, ƙarin girma da kuma ladabtar da ƙananan jami’an ‘yan sanda na jihohi.

8. ‘Yancin gudanar da aiki

Domin hana yiwuwar cin zarafi na siyasa da amfani da iko ba daidai ba, dokar ta bai wa shugabannin ‘yan sanda ‘yancin gudanar da ayyukansu.

Dole ne a bayar da dukkan umarnin zartarwa da rubuce, kuma jami’ai na da ikon ƙin bin umarnin da ya saɓa wa doka.

Kara karanta wannan

An fara sabuwar fafutukar neman karin albashi mai tsoka a Najeriya

Haka kuma za a kafa sassan karɓar koke-koken jama’a domin sauraron ƙorafe-ƙorafe game da ayyukan 'yan sandan jihohi.

9. Hadin gwiwar shekara 2

Kwamitin haɗin gwiwa wanda ya ƙunshi wakilan gwamnatin tarayya da jihohi zai kula da miƙa ragamar gudanarwa ga jihohin cikin tsawon watanni 24.

Za a sake raba jami’an da ake da su bisa wuraren aikinsu na yanzu, yayin da matsayinsu, fansho da sharuɗɗan aikinsu za su kasance a karkashin doka.

10. Daidaita kundin tsarin mulki

Aiwatar da dokar zai dogara ne kaco-kam kan yin gyare-gyare cikin gaggawa ga kundin tsarin mulkin Najeriya ba shekarar 1999.

Dole ne majalisar tarayya ta gyara jadawali na uku tare da sauya jerin hukunce-hukunce keɓaɓɓu domin a mayar da harkokin ‘yan sanda zuwa jerin hukunce-hukuncen haɗin gwiwa.

Maganar dan majalisar Amurka

A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa ɗan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya yi maraba da zartar da dokar kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya.

Moore Ya bayyana matakin a matsayin babban ci gaba wajen inganta tsaro da kare al’ummomin da ke cikin haɗari a fadin Najeriya.

Dan majalisar ya kara da cewa ya ɗauki tsawon lokaci yana kira a bayyane da boye domin ganin an kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng