
Hukumar Jin dadin yan sanda







Dokar hana zirga-zirga a Gombe daga 12:00 na dare zuwa 5:00 na asuba na hana bata-gari aikata laifuffuka. Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi karin bayani.

Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari gidan jami’in ‘yan sanda a Buni Yadi, suka kashe ‘ya’yansa biyu, suka kona gawarwakinsu da gidan, lamarin ya jefa tsoro.

Rundunar 'yan sanda ta karyata jita-jitar cewa 'yan bindiga ne suka kashe tsohon shugaban NIS. Rundunar ta ce Parradang ya mutu a dakin otel bayan ya shiga da wata.

Safiyanu Dalhatu ya kashe mahaifiyarsa da tabarya a Bauchi. Yanzu dai 'yan sanda sun kama shi, sun kwace makamin, kuma ana shirin gurfanar da shi a kotu.

‘Yan sandan jihar Imo sun kama masu safarar yara, inda suka ki karbar cin hancin N1m, kuma suna ci gaba da bincike kan wata babbar cibiyar safarar yara.

Rundunar 'yan sanda sanda ta kama Alhassan Isa da ake zargi da satar mota a Jigawa, kuma ya amsa laifinsa, yayin da ake shirin gurfanar da shi gaban kotu.

Rundunar 'yan sanda ta ayyana Hafsat Kabir da Baba Sule a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo. 'Yan kasa na iya cafke su tare da mika su ga hukuma mafi kusa.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwar cewa za ta fara daukan aikin 'yan sanda a shekarar 2025. An bayyana matakin da masu neman aiki za su bi.

Wasu da ake zargi da kisan dan majalisar Anambra sun tsere daga hannun ‘yan sanda. Kwamishinan 'yan sanda ya tura jami’ai don kamo su tare da hukunta masu sakaci.
Hukumar Jin dadin yan sanda
Samu kari