Abin da Gwamnoni za Su Iya Yi da ‘Yan Sandan Jihohi da Wanda aka Hana Su

Abin da Gwamnoni za Su Iya Yi da ‘Yan Sandan Jihohi da Wanda aka Hana Su

Yayin samar da dokar 'yan sandan jihohi a Najeriya, majalisar tarayya ta dauki matakai da dama domin hana gwamnoni amfani da su domin cimma muradun siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sabuwar dokar 'yan sandan jihohi da shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar dokoki ta kasa, wadda majalisar dattawa ta amince da ita, na iya zama doka kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Tun bayan amincewar majalisa da dokar, 'yan siyasa, masana da masu sharhi suka rika korafi kan yiwuwar amfani da 'yan sandan jihohi ba bisa ka'ida ba.

Gwamnonin jihohi da 'yan sanda
Gwamnonin jihohi a hagu da dakarun 'yan sanda a dama. Hoto: Bologi Ibrahim|Nigeria police Force
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku wasu matakai da majalisun tarayya suka dauka domin hana gwamnoni amfani da 'yan sandan ba bisa ka'ida ba.

Fara aikin 'yan sandan jihohi

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu bayan kai hari a Katsina

Vanguard ta wallafa cewa dokar ta ce kowace jiha za ta fara ne da kafa dokarta ta 'yan sanda kafin ta kafa rundunar 'yan sandan jihar, kuma wannan dokar dole ne ta cika ƙa'idojin da majalisar dokoki ta kasa ta gindaya.

Idan aka samar da su, 'yan sandan jihohi za su kasance da ikon gudanar da ayyuka kamar haka:

  • Aiwatar da dokokin jiha
  • Tabbatar da tsaron jama'a da zaman lafiya
  • Hana aikata laifuffuka a cikin iyakar jihar
  • Gudanar da sauran ayyukan tsaro na cikin gida
Yan sandan Najeriya na farautar masu laifi
Dakarun 'yan sandan Najeriya a bakin aiki a Abuja. Hoto: FCT Police Command
Source: Facebook

Sai dai, rahotanni sun nuna cewa 'yan sandan tarayya za su iya shiga cikin harkokin tsaron jiha idan doka da oda sun rushe gaba ɗaya.

Hakan zai faru ne idan gwamnan jihar ya nemi hakan, ko kuma idan rundunar 'yan sandan jihar ba ta da ƙarfin gudanar da aikinta saboda matsalolin aiki, kuɗi ko gudanarwa.

Gwamna vs 'yan sandan jihohi

Gwamnonin jihohi za su kasance da ikon naɗa kwamishinonin 'yan sanda na jihohinsu daga cikin jami'an 'yan sandan jihar da ke aiki, kuma za su iya ba su umarni kai tsaye.

Sai dai naɗin da gwamna ya yi ba zai tabbata ba har sai majalisar dokokin jihar da hukumar kula da ayyukan 'yan sanda sun amince da shi.

Kara karanta wannan

An shiga jimami da 'yan bindiga suka kashe babban limami da wasu mutane a Sokoto

Mai magana da yawun majalisar dattawa, Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan a wata hira da tashar Arise News inda ya kwatanta tsarin da yadda ake naɗa manyan alƙalan jihohi.

gwamnonin jihohi a wajen taro
Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya a Abuja. Hoto: Abdul No Shaking
Source: Facebook

Yemi Adaramodu ya ce:

“Idan gwamnoni sun naɗa kwamishinonin 'yan sanda, za a mayar da sunayensu zuwa hukumar kula da ayyukan 'yan sandan tarayya, wadda za ta duba tarihin aiki da cancantar duk jami'in da aka zaɓa kafin ya zama kwamishinan 'yan sandan jihar.”

Batun takawa gwamnoni burki

BBC ta rahoto cewa kudirin ya kuma tanadi wasu matakan kariya domin hana gwamnoni amfani da rundunar ba bisa ka'ida ba. Sun haɗa da:

1. Ba wajibi ba ne Kwamishinan 'yan sandan jiha ya aiwatar da duk wani umarni da ya saɓa wa doka daga gwamna, maimakon haka zai kai rahoto ga majalisar 'yan sanda ta kasa.

2. Sashe na 17(7) ya tanadi cewa kwamishinan ‘yan sandan jiha ba zai kama, tsare, binciken wani mutum ko amfani da ƙarfi kan jam'iyyar siyasa ko ƙungiya ba saboda kawai sun soki gwamnati, sai dai idan hakan ya kasance bisa tanadin doka.

Wajen da ake yi wa 'yan sanda horo
Jami'in 'yan sanda na yi wa masu neman shiga aiki bayani. Hoto: Gombe State Police Command
Source: Facebook

3. Majalisar dokoki ta kasa za ta ci gaba da tsara ƙa'idojin ɗaukar ma'aikata, horaswa, tantancewa, ƙara matsayi da ladabtar da jami'an 'yan sanda domin tabbatar da ƙwarewa da riƙon amana.

Kara karanta wannan

Jirgin sojojin Najeriya ya far wa yan bindiga kimanin 200, ya musu gagarumar illa a Neja

4. 'Yan sandan tarayya za su iya shiga idan an samu take haƙƙin ɗan Adam mai tsanani, barazanar tsoratar da masu zaɓe, ko kuma idan tsaron ƙasa ya shiga haɗari.

5. A duk lokacin da 'yan sandan tarayya za su shiga harkokin jiha, shugaban kasa ne kaɗai ke da ikon ba da izinin hakan, kuma dole ne izinin ya kasance a rubuce.

An soki kafa 'yan sandan jihohi

A wani labarin, mun kawo muku cewa jagora a jam'iyyar NDC, Buba Galadima ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan kafa 'yan sandan jihohi.

Buba Galadima ya bayyana cewa 'yan sandan jihohi ba za su iya magance matsalar rashin tsaro da 'yan sandan tarayya suka gaza ba.

A karkashin haka ya yi zargin cewa shugaban kasa da gwamnoni suna son yin amfani da 'yan sandan jihohi ne saboda manufar siyasar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng