Umarnin da Fadar Shugaban Kasa Ta Ba DSS, EFCC kan Batun Ma'aikatar Bogi

Umarnin da Fadar Shugaban Kasa Ta Ba DSS, EFCC kan Batun Ma'aikatar Bogi

  • Ana ci gaba da muhawara kan batun ma'aikatar bogi da wani mai suna Adeniyi Adeyemi ke jagoranta ba tare da sanin gwamnati ba
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Adeniyi gogaggen dan damfara ne wanda yake kokarin bata sunan Femi Gbajabiamila
  • Ta bayyana cewa an ba da umarni ga hukumomin DSS, 'yan sanda da EFCC kan lamarin wanda ke da alamar tambayoyi masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta ba hukomin DSS, EFCC umarni kan dambarwar hukumar bogi ta PFIPC.

Fadar shugaban kasa ta umarci DSS, EFCV da su zakulo mutanen da ke cikin gwamnati da ke aiki tare da Adeniyi Adeyemi don gudanar da hukumar PFIPC domin a gurfanar da su.

Fadar shugaban kasa ta umarci a yi bincike
Adeniyi Adeyemi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai da hulda da jama'a, Temitope Ajayi, wanda ya bayyana hakan a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Juma'a, 3 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Akwai bata gari a gwamnati

Fadar shugaban kasar ta yi zargin cewa akwai masu haɗin baki na cikin gida da ke ba Adeniyi damar yin kamfen ɗin ɓata suna da ake yi wa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Ajayi ya zargi Adeniyi da kasancewa "gogajen ɗan damfara" wanda yake amfani da basira wajen amfani da tunanin al'umar Najeriya game da cin hanci da rashawa don kare kansa daga fuskantar shari'a ta hanyar jawo sunan Gbajabiamila a cikin sana'arsa ta zamba ta biliyoyin nairori.

Wane umarni aka ba DSS, EFCC?

Ya ce an ɗaurawa masu bincike daga hukumomin DSS, 'yan sanda da EFCC alhakin tona asirin cikakken girman haɗin gwiwar da ya ba Adeniyi damar yin abubuwan da ya yi.

Abubuwan da ya yi sun hada da ƙirƙirar takardun naɗin shugaban ƙasa na bogi, gudanar da asusun banki guda 34 da sunayen hukumomin gwamnati na bogi, karɓar baƙuncin jakadun ƙasashen waje da kuma buɗe asusun CBN.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Gbajabiamila: Jam'iyyar NDC ta mika bukata ga Tinubu da EFCC

“Abin da ba a shakka a kai shi ne cewa masu haɗin baki na cikin gwamnati ne suka ba Adeniyi damar takawa har zuwa wannan matakin. Wannan shi ne ainihin abin da masu bincike daga DSS, 'yan sanda da kuma EFCC dole ne su tona asirinsa yanzu."
“Dole ne a tarwatsa gungun masu laifi da ke cikin hukumomin da abin ya shafa, kuma kowa da aka samu yana da hannu a ciki ya kamata a kama shi tare da gurfanar da shi.”
“A Najeriya, zargi mafi sauƙi da mafi gamsarwa da kowa zai iya jefawa jami'in gwamnati shi ne cin hanci da rashawa."
“Matthew Adeniyi ya fahimci tunanin al'ummar Najeriya kuma yana amfani da shi cikin basira don kare kansa."
"Shi gogajen ɗan damfara ne mara gyaruwa wanda yake ƙoƙarin jawo sunan shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, cikin sana'arsa ta laifi. Shugaban ma'aikatan shi ne kawai mafita ta ƙarshe a gare shi."

- Temitope Ajayi

Adeniyi Adeyemi na fuskantar zarge-zarge
Adeniyi Adeyemi da ake ta cece-kuce a kansa kan ma'aikatar bogi Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Atiku ya ba Tinubu wa'adi kan ma'aikatar bogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya yi magana kan batun ma'aikatar bogi.

Atiku ya ba Shugaba Bola Tinubu wa'adin kwanaki bakwai da ya bayar da umarnin gudanar da bincike na gaskiya, kan badakalar hukumar PFIPC.

Ya yi gargaɗin cewa rashin yin hakan zai ƙara rura wutar zargin jama'a na cewa wasu manyan mutane masu iko a gwamnati sun ci gajiyar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com