Abin da Sabuwar Dokar Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya ta Kunsa
FCT, Abuja - Fiye da shekaru 20 fafutukar neman kafa rundunar 'yan sandan jihohi ta kasance ɗaya daga cikin batutuwa mafi dambarwa da kawo rarrabuwar kai a cikin muhawarar siyasa da tsarin mulki ta Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Wasu na ganin wannan ita ce mafita da aka daɗe ana jiran ta ga matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta'azzara a ƙasar. Wasu kuma suna fargabar cewa hakan na iya damkawa gwamnoni gagarumin iko wanda za su iya amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba domin cimma manufofin siyasa.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta kawo rahoton cewa a ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026, muhawarar ta matsa zuwa matakin kusa da zama doka.
Majalisa ta amince a kafa 'yan sandan jihohi
Majalisar Wakilai ta amince da gagarumin rinjaye kudirin da zani yi gyara ga tsarin mulki wanda ke neman kafa rundunar 'yan sandan jihohi a faɗin tarayyar ƙasar.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja
Hakazalika, Majalisar Dattawa ma ta amince da kudirin a ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026, kamar yadda rahoton jaridar The Punch ya nuna.
Idan har aka samu bambance-bambance tsakanin nau'ikan da Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka amince da su, za a kafa wani kwamiti domin daidaita su kafin a tura kudirin na ƙarshe zuwa ga jihohi, kamar yadda tsarin mulki ya buƙata.
Dole ne aƙalla Majalisun Dokoki na jihohi 24 daga cikin 36 su amince da shi, kuma shugaban ƙasa ya sanya hannu kafin ya zama ɓangare na kundin tsarin mulki.
Menene abubuwan da kudirin ya kunsa?
Yayin da kudirin ya ƙunshi sauye-sauyen tsarin mulki da dama, sharuɗɗa da dama sun fito fili saboda tasirin da suke da shi a kan yadda za a gudanar da tsaro a faɗin tarayyar ƙasar.
1. Tsarin 'yan sanda guda biyu
Wataƙila mafi girma cikin tanadin shi ne ƙirƙirar tsarin aikin ɗan sanda guda biyu wanda ya ƙunshi 'yan sandan tarayya da 'yan sandan jihohi.
Hakan zai kawo ƙarshen tsarin na yanzu wanda a ƙarƙashinsa rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) ita ce kaɗai hukumar 'yan sanda da aka sani a ƙasar.

Kara karanta wannan
Sabuwar kungiyar 'yan damfarata bulla a Kebbi, gwamnati ta bayyana barnar da suke yi
Sai dai kuma, jihohi ba za su fara ayyukan 'yan sanda kai-tsaye ba. Kafin hukumar 'yan sanda ta jiha ta fara aiki, dole ne ta ƙaddamar da dokar kafa rundunar kuma ta cika dokokin tarayya.
2. Gwamnoni ne za su naɗa kwamishinonin 'yan sandan jiha
A ƙarƙashin kudirin, kowace hukumar 'yan sanda ta jiha za ta kasance ƙarƙashin jagorancin wani kwamishinan 'yan sanda da gwamna ya naɗa.
Sai dai kuma, naɗin ba zai kasance kacokan a kan ra'ayin gwamna ba. Zai haɗa da majalisar 'yan sandan kasa kuma yana buƙatar amincewar Majalisar Dokoki ta jiha.
Wannan tanadin yana neman tabbatar da cewa tsarin naɗin ya ƙunshi dabarun bincike da daidaitawa.
3. Kwamishinonin 'yan sanda za su iya ƙalubalantar umarnin gwamnoni
Ɗaya daga cikin tanadin an tsara shi ne domin magance fargabar cewa gwamnoni na iya amfani da 'yan sandan jiha don manufofin siyasa.
Kudirin ya ba wa kwamishinan 'yan sanda na jiha damar ƙalubalantar umarnin da ake ɗauka a matsayin ba na doka ba ne ko kuma wanda bai dace da ƙa'idodin aikin 'yan sanda da aka kafa ba.
Inda irin wannan takaddama ta taso, za a mika batun ga majalisar 'yan sandan kasa, wadda shawararta za ta kasance ta ƙarshe.

Kara karanta wannan
Ardo Risku: Mutane 10 da ake zargi da kisan shugaban Miyetti Allah sun shiga hannu
4. Abuja tana iya tsoma baki a jihohi har yanzu
Sabanin ra'ayoyin cewa 'yan sandan jiha za su yi aiki gaba ɗaya ba tare da dogaro ga kowa ba, kudirin ya kawo rawar da 'yan sandan tarayya za su taka.
Za a ba da damar tsoma bakin tarayya idan har aka samu rugujewar doka da oda baki ɗaya, ko kuma idan gwamna ya nemi taimako, ko kuma idan hukumar 'yan sanda ta jiha ta gaza yin aiki saboda matsalolin gudanarwa, na aiki, ko na kuɗi. Ko a lokacin ma, za a buƙaci amincewa daga majalisar 'yan sandan kasa.
5. Gwamnatin tarayya tana iya ɗaukar nauyin 'yan sandan jiha
Batun kuɗi ya kasance ɗaya daga cikin manyan damuwar da ke tattare da batun kafa 'yan sandan jihohi.
Domin magance wannan, kudirin ya ba wa gwamnatin tarayya ikon samar da tallafi da taimakon kuɗi ga hukumomin 'yan sandan jihohi, bisa shawarwarin mjalisar 'yan sanda ta kasa da amincewar Majalisar Tarayya.
6. Za a samar da majalisar 'yan sanda ta kasa mai iko

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: PRP ta kawo cikas a shirin ƙirƙiro rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya
Kudirin yana ba da shawarar faɗaɗa majalisar 'yan sanda ta kasa za ta ƙunshi wakilan gwamnatin tarayya da na jihohi, jami'an 'yan sanda da suka yi ritaya, hukumomin haƙƙin ɗan adam, ƙungiyoyin ƙwadago, shugabannin gargajiya, lauyoyi, da 'yan jarida.
Majalisar za ta zama babbar cibiyar daidaita ayyukan 'yan sanda a faɗin ƙasar baki ɗaya. Ikon ta zai haɗa da naɗe-naɗe, ladabtarwa, kafa ƙa'idodi, sanya idanu, da kuma daidaitawa tsakanin hukumomin 'yan sanda na tarayya da na jiha.
7. Kowace jiha za ta kafa hukumar kula da 'yan sanda
Kudirin ya kuma buƙaci kowace jiha da ta kafa hukumar kula da 'yan sanda ta jiha. Hukumar za ta kasance da alhakin ɗaukar ma'aikata, ladabtarwa da kula da ma'aikata a cikin hukumar 'yan sanda ta jiha.
Za ta ba da shawara manyan jami'ai da za a nada mukamai yayin da take gudanar da iko na kai-tsaye a kan jami'an da ke ƙasa da matsayin mataimakin kwamishinan 'yan sanda.
Sashen da watakila zai fi kawo muhawara
Kudirin ya ƙunshi matakan kariya da dama, sharuɗɗan da ke ba wa gwamnoni ikon naɗa kwamishinonin 'yan sandan jihohi yana da yuwuwar kasancewa ɗaya daga cikin sassan da suka fi kawo ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan
Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa
Masu suka sun daɗe suna jayayya cewa ana iya amfani da 'yan sandan jiha a matsayin makami na yaƙi da abokan hamayya na siyasa, musamman lokacin zaɓe.
Sai dai kuma, masu goyon baya sun mayar da martani cewa buƙatar kudirin na shigar da majalisar 'yan sanda ta kasa, amincewar majalisar dokoki, da kuma hanyoyin sanya idanu masu zaman kansu suna samar da isassun hanyoyi domin hana amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba.

Source: Facebook
Masu tsara sabon kudirin sun bayyana cewa sun yi ƙoƙarin magance waccan damuwa. A ƙarƙashin kudirin, kowace hukumar 'yan sanda ta jiha za ta kasance ƙarƙashin jagorancin wani kwamishinan 'yan sanda da gwamna ya naɗa.
Sai dai kuma, naɗin ba zai kasance kacokan a kan ra'ayin gwamna ba. Dole ne wanda za a nadan a dauko ta hanyar tsarin da ya haɗa da majalisar 'yan sanda ta kasa kuma Majalisar Dokoki ta jiha ta amince da shi.
Mafi mahimmanci, kudirin ya samar da kariya daga umarnin da ƙila ba na doka ba ne. Idan kwamishina ya yi amanna cewa umarnin gwamna ya keta ƙa'idodin aikin 'yan sanda ko doka, ana iya mika batun ga majalisar 'yan sanda ta kasa domin duba shi.
Shawarar majalisar za ta zama tilas ga kowa. Wannan tanadin yana iya zama wani muhimmin hanyar hana katsalandan na siyasa. Ko zai yi aiki a aikace, lokaci ne zai nuna hakan.
Shin jihohi za su iya kuwa?
Bayan siyasa, batun kuɗi yana iya zama babbar cikas ga aiwatarwa. Kafawa da kuma kula da hukumar 'yan sanda abu ne mai tsada sosai.
Albashin ma'aikata, ɗaukar ma'aikata, horarwa, kayan aiki, tsarin sadarwa, dakunan binciken kimiya na gano laifuffuka, tsarin bayanan sirri, da kuma dabarun tafiyar da ayyuka suna buƙatar kudi masu tsoka.
Jihohi da dama suna fafutuka wajen cika wajibai na yanzu, ciki har da biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
PRP ta nuna adawa da 'yan sandan jihohi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PRP mai adawa ta nuna rashin amincewarta da shirin da ake yi na kafa 'yan sandan jihohi.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce PRP ta tana matukar damuwa da yunkurin kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ba ta da isasshen karfi da goyon bayan jama’a domin jagorantar irin wannan babban sauyi a tsarin tsaron kasar.
Asali: Legit.ng
