Bayan Ya Ci Gabza, DSS Ta Saki Bakatsine da ake Zargi da Sace Daliban Oyo
- Hukumar DSS ta saki Mustapha Marwana, wani kafinta ɗan asalin jihar Katsina, wanda aka kama da zargin alaka da 'yan ta'addan Ansaru
- An kama Marwana ne bisa zargin cewa ya na da hannu a sace ɗalibai da malamai a yankin Oriire da ke kusa da Ogbomoso a Jihar Oyo
- Bayan bincike ya wanke shi daga zargin, hukumar DSS ta sake shi sannan ta ba shi miliyoyin Naira a matsayin diyyar tsare da aka yi ba tare da laifi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Oyo – Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta saki wani mutum mai suna Mustapha Marwana, wanda aka kama bisa zargin yana da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru.
An kama Marwana, wanda yake sana’ar kafinta kuma ɗan asalin Jihar Katsina, ne a lokacin da ake bincike kan sace ɗalibai da malamai a yankin Oriire da ke ƙaramar hukumar Oriire, kusa da Ogbomoso a Jihar Oyo.

Source: Twitter
Kafar Channels ta wallafa cewa wata majiya daga DSS ta tabbatar da cewa an saki mutumin ne bisa umarnin Darakta-Janar na hukumar, Oluwatosin Ajayi.
DSS ta saki Bakatsine kan zargin ta'addanci
The Cable ta ruwaito cewa bayan tabbatar da rashin laifinsa, hukumar DSS ta ba Marwana N3m a matsayin diyya domin taimaka masa wajen komawa rayuwarsa ta yau da kullum.
A watan Yuli, 2026 wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutane uku hukuncin daurin rai da rai saboda hannu a sace ɗalibai da malamai a wata makaranta da ke Oriire.
Mutanen da aka yankewa hukuncin su ne Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid; Yunusa Musa, wanda ake kira Yunusa bin Musa; da Shamsu Adamu Sani, wanda aka fi sani da Abu Itisar.
An gurfanar da wasu kan ta'addanci
An gurfanar da mutanen uku kan tuhume-tuhume 10 da suka shafi ta’addanci, garkuwa da mutane, ɓoye bayanai, tunzura mutane da kuma haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Source: Original
A ranar 15 ga Mayu, 2026 wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantu uku a ƙaramar hukumar Oriire, inda suka sace ɗalibai 39 da malamai bakwai, ciki har da shugaban ɗaya daga cikin makarantun.
Bayan kwanaki kaɗan, masu garkuwar sun kashe Michael Oyedokun, ɗaya daga cikin malaman da aka sace. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta tare da zanga-zangar neman a ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
An tsare tsohon jami'in DSS
A baya, mun kawo labarin cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gurfanar da tsohon jami'inta a kotun tarayya bisa zargin shiga IPOB da kuma tallafa wa kungiyar tayar da kayar bayan.
Ana zarginsa da yada sakonni a kafafen sada zumunta domin jan hankalin jama'a su goyi bayan kungiyar aware ta IPOB, lamarin da DSS ta ce ya saba dokokin yaki da ta'addanci.
Wanda ake zargin ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, yayin da kotu ta tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje tare da sanya ranar 29 ga Oktoba, 2026 domin ci gaba da zama kan batun.
Asali: Legit.ng

