Gwamna Dauda Ya Yi Maganar Sulhu da 'Yan Bindiga bayan Ya Je Ta'aziyya

Gwamna Dauda Ya Yi Maganar Sulhu da 'Yan Bindiga bayan Ya Je Ta'aziyya

  • Gwamna Dauda Lawal ya sake jaddada cewa gwamnatin Zamfara ba za ta yi sulhu ko tattaunawa da masu aikata laifuffuka ba
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ƙaramar hukumar Bungudu bayan harin 'yan bindiga da aka kai
  • Ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafa wa waɗanda suka jikkata tare da ƙoƙarin ceto duk mutanen da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu ko tattaunawa da masu aikata laifuffuka ba.

Gwamna Dauda Lawal ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta mika kai ga 'yan bindiga masu kashe mutane ba.

Gwamna Dauda ba zai yi sulhu da 'yan bindiga ba
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Rarara ya kira ruwa, PDP ta yi masa tatas kan taba Farfesa Pantami

Sanarwar ta ce gwamnan ya sake jaddada wannan matsaya ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya zuwa ƙaramar hukumar Bungudu bayan harin 'yan bindiga da aka kai a makon da ya gabata.

Dauda Lawal ya yi ta'aziyya ga al'ummar Bungudu

Da farko, gwamnan ya ziyarci fadar Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, inda ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a fadin Zamfara.

"Na zo ne domin nuna alhini da jajantawa iyalan waɗanda suka rasu, Mai Martaba Sarki da kuma al'ummar Bungudu sakamakon hare-haren 'yan bindiga da aka kai a makon jiya."
"Wannan jarabawa ce daga Allah Maɗaukakin Sarki, kuma da yardarsa za mu yi nasara a kanta. Gwamnatin jiha na ci gaba da ware dukkanin kayan aiki da albarkatun da suka dace domin kawo ƙarshen matsalar 'yan bindiga."
"Ina roƙon kowa da ya ci gaba da yin haƙuri, domin wannan lamari na buƙatar juriya da kuma yawaita addu'a." In ji shi

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Gwamna Dauda Lawal ya kuma yi addu'ar Allah Ya ba iyalan waɗanda suka rasa rayukansu haƙurin jure wannan rashi, tare da roƙon Allah Ya gafarta wa mamatan.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da dukkan tallafin da ya dace ga waɗanda suka jikkata, tare da yin iyakar ƙoƙarinta domin ganin an kuɓutar da duk mutanen da aka yi garkuwa da su.

Sarkin Bungudu ya yabawa gwamnan

Da yake mayar da martani, Sarkin Bungudu ya gode wa Allah da Ya ba Zamfara gwamna mai nuna damuwa kan halin da jama'a ke ciki tare da ɗaukar matakan magance matsalar tsaro.

"A matsayina na mamba a kwamitin tsaron jihar, na san irin ƙoƙarin da gwamna ke yi. Ina da yakinin cewa za mu shawo kan matsalar 'yan bindiga."
"Muna godiya da wannan ziyarar ta'aziyya. Ta ƙara wa al'ummar ƙaramar hukumar Bungudu ƙwarin gwiwa." In ji shi.

Bayan ziyarar fadar sarkin, Gwamna Dauda Lawal ya kuma kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Bello Umar Bungudu da sauran waɗanda suka rasa 'yan uwansu sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

Gwamna Dauda ya je ta'aziyya
Gwamna Dauda Lawal tare da sarkin Bungudu yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kashe dan siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe tsohon kansilan mazabar Rim da ke ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau, Daniel Danjuma Chong,

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Torok da ke yankin Rim, inda maharan suka buɗe wuta kan mazauna yankin kafin su tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng