Atiku Ya Dura Osun, Ya Bukaci a Murkushe APC da Dan Takarar Ta
- Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci al'ummar Osun su zaɓi ɗan takarar gwamna na ADC, Najeem Salaam, zaben jihar
- Atiku ya ce jam'iyyar ADC ta bambanta da APC, Accord da sauran jam'iyyun siyasa, yana mai cewa mafi kyawun ‘yan Najeriya suna cikinta
- Tsohon mataimakin shugaban ya tuna da irin goyon bayan da al'ummar Osun suka ba shi a baya, yana neman su sake mara wa ADC baya a zaɓen gwamnan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun – Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya roƙi al'ummar jihar Osun da su zaɓi ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC, Najeem Salaam, a zaɓen da za a gudanar ranar Asabar.
Atiku ya yi kiran ne ranar Litinin yayin babban taron yaƙin neman zaɓen ADC da aka gudanar a Osogbo, babban birnin jihar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da taron da ADC ta yi a jihar Osun ne a wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Bambancin ADC da jam'iyyu
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya ce jam'iyyar ta bambanta da APC, Accord da sauran jam'iyyun siyasa.
Ya ce al'ummar jihar ba za su yi nadamar zaɓar ADC ba, yana mai neman su bai wa Salaam goyon baya a zaɓen gwamna.
The Cable ya wallafa cewa Atiku ya ce:
"Na zo yau ne domin sake roƙonku da ku zaɓi ADC. Mafi kyawun ‘yan Najeriya suna cikin ADC a yau."
Ya ƙara da cewa ya zo da kansa domin godiya ga al'ummar Osun bisa irin goyon bayan da suka ba shi a baya.
Atiku ya tuna da alherin Osun
Tsohon mataimakin shugaban ya ce wannan shi ne karo na huɗu da ya tsaya a kan wannan dandali a Osun, inda ya ce a duk lokacin da ya zo, al'ummar jihar sun ba shi kuri'unsu.
Ya ce ba zai taɓa mantawa da irin wannan goyon baya ba, yana mai tunawa da ziyarar da ya kai jihar a lokutan baya.
Atiku ya ce ya taɓa yi wa gwamnan jihar na yanzu, Ademola Adeleke, yaƙin neman zaɓe, sannan ya sake komawa jihar yayin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.

Source: Facebook
Ya ce a dukkan lokutan biyu, al'ummar jihar sun mara masa baya, kuma Atiku ya buƙaci al'ummar Osun da su sake nuna goyon bayansu ta hanyar zaɓar jam'iyyar ADC a zaɓen gwamna mai zuwa.
An zargi APC da shirin magudi
A wani labarin, mun ruwaito cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen Imole ya yi zargin cewa jam'iyyar APC na shirin matsa wa INEC lamba domin dakatar da zaɓe da tsakar rana a wasu ƙananan hukumomin Osun.
Kwamitin ya ce ana zargin shirin ne domin shafar ƙananan hukumomin da ake ganin su ne cibiyoyin siyasar Gwamna Ademola Adeleke.
Ya bayyana cewa matakin na iya hana dubban masu kaɗa kuri'a damar yin amfani da haƙƙinsu, tare da yin barazana ga sahihancin zaɓen.
Asali: Legit.ng

