Sarkin Kano Sanusi II Ya soki Majalisa, Ya Haska Barnar da Aka yi a Gwamnati
- A dokar kasa, Gwamnatin tarayya ba za ta iya cin bashin fiye da 5% na kudin shiga da Najeriya ta samu ba daga hannun CBN
- Muhammadu Sanusi II wanda ya yi gwamnan babban banki ya zargi ‘yan majalisa da kyale Gwamnatin Najeriya ta karya wannan doka
- Sarkin Kano na 16 ya ce akwai bambanci tsakanin yadda abubuwa suke tafiya a yau da kuma zamanin da ya rike bankin CBN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II bai gamsu da yadda ‘yan majalisar Najeriya suke aiki ba musamman a karkashin gwamnatin yau.
Muhammadu Sanusi II ya yi wasu maganganu ne a daidai lokacin da ake zargin ‘yan majalisa da zama ‘yan amashin shatan masu rike da madafu.

Source: Getty Images
Muhammadu Sanusi II ya yi magana a NILDS
The Cable ta rahoto wani bangare na jawabin da Khalifa Muhammad Sanusi II, PhD da ya yi a wajen wani taro da aka shirya a cibiyar NILDS a Abuja.

Kara karanta wannan
Shekaru da barin CBN, Sanusi II ya fayyace hakikanin alakarsa da Yar’adua da Jonathan
Mun fahimci an yi zaman ne game da abin da ya shafi harkar kudi a yammacin Afrika, aka kuma yi duba da kyau game da abin da ya shafi Najeriya.
A taron da aka yi, Sarkin Kano ya koka game da yadda ‘yan majalisar Najeriya suke aiki a yau.
A maimakon a ga sanatoci da ‘yan majalisa sun matsa wa bangaren zartarwa, Muhammadu Sanusi II ya zarge su da zama yan a bi Yarima – a sha kida.
“Kana da majalisa da ya kamata ta rika yin dokoki, ta rika taka wa shugabanni burki.
Idan majalisa ba za ta iya taka wa shugabanni burki ba, sai ta zama bangaren masu zartarwa, wannan ba majalisa mai karfi ba ce.
Basaraken ya fadakar da mahalarta wannan taro cewa ya kamata lura da abin da yake faruwa, tashar TV Platinum ta wallafa bidiyon a Facebook.
“Saboda haka ya kamata cibiyar da ke nazarin ayyukan majalisa ta kula da wannan.”
- Muhammadu Sanusi II

Source: Getty Images
Sanusi II ya bukaci bangarorin gwamnati su zauna daram
A rahoton Nigerian Lawyer, an ji cewa sarkin ya yi gargadi cewa dole sai hukumomi sun tsaya da kafafunsu ne sannan za a iya samun cigaba a kasa.
Ya ce tafiyar da gwamnati ba a gine-gine ko sunaye ba ne, sai an bar kowa ya yi aikinsa da kyau ba tare da katsalandan daga masu rike da mukamai ba.
Tsohon gwamnan CBN ya zargi Gwamnatin tarayya da yin shekaru tana karya doka wajen cin bashin daga hannun babban bankin Najeriya a shekarun baya.
An yi shekaru takwas, akwai kwamitin da ke lura da harkokin banki a Majalisar dattawa da majalisar wakilai
Majalisar tarayya ta kawo doka, dokar nan ta ce ba za ku iya bada aron fiye da 5% na kudin shigan bara ba
An yi wa dokar nan hawan kawar, ina majalisar tarayya?
- Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya ce a lokacinsa duk wani abin da ya faru a kan kira shi majalisa ya yi bayani, abin da ya daina gani a karkashin gwamnatocin APC mai ci.
Duk tulin kwamitocin da ake da su, ya ce ‘yan majalisa da masana tattalin arziki sun yi gum maimakon ganin cewa an bi dokokin da aka tsara.
An samu shugabannin majalisa a Najeriya
Idan za a tuna, a watan Yunin 2023 ne aka rahoto Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas suka zama shugabannin majalisar dattawa da na wakilai.
A lokacin da aka rantsar da majalisar, Bamidele, Dave Umahi, da Sanata Ali Ndume suna cikin sabbin jagororin da aka sanar bayan an kammala zabe.
Opeyemi Bamidele ya zama shugaban masu rinjaye, Ali Ndume ya zama babban mai ladabtarwa, da Simon Davou kuma ya zama shugaban marasa rinjaye.
Asali: Legit.ng

