Sheikh Sani Rijiyar Lemo Ya Zamo Farfesan Hadisi a Jami'ar Bayero

Sheikh Sani Rijiyar Lemo Ya Zamo Farfesan Hadisi a Jami'ar Bayero

  • Jami’ar Bayero ta Kano ta tabbatar da karin girman Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo zuwa matsayin Farfesa
  • Malamin ya kasance kwararre a Hadisin Manzon Allah (SAW) tare da gagarumin suna a ilimin addinin Musulunci
  • Al’umma a ciki da wajen Najeriya sun fara taya shi murna tare da yi masa addu’ar fatan alheri a kan sabon matsayin da ya samu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Babban Malami a Jami’ar Bayero ta Kano, Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya samu karin girma zuwa Farfesa a Hadisin Manzon Allah (SAW).

Karin girman alama ce da ke nuna hazakar malamin a fannin ilimin da ilmantarwa a ciki da wajen jami'ar.

Legit ta samu sanarwar ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafin Sheikh Sani Rijiyar Lemo na Facebook a yau Juma'a, 27 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ɓatan malami, yan bindiga sun bindige malamin addini, an bukaci addu'o'i

Rijiyar Lemo
Sheikh Rijiyar Lemo ya zamo Farfesa a Hadisi. Hoto: Dr. Muhd Sani Umar R/lemo
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta samu sanarwar ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafin Sheikh Sani Rijiyar Lemo na Facebook a yau Juma'a, 27 ga watan Disamba.

Karin bayani kan Farfesa Sani Rijiyar Lemo

Sheikh Muhammad Sani Umar R/Lemo ya shahara wajen koyarwa, rubuce-rubuce, da wallafa littattafai a fannin addinin Musulunci.

Shehin malamin ya yi karatu a Jami’ar Musulunci ta Madina, inda ya samu horo mai zurfi a ilimin Hadisi.

Ya rike mukamai da dama a Jami’ar Bayero ta Kano tare da gudanar da karatuttuka a ciki da wajen jihar Kano, wanda hakan ya sa ya kasance daya daga cikin manyan malaman Najeriya.

Rijiyar Lemo

An taya Farfsesa Rijiyar Lemo murna

Bayan sanarwar karin girman malamin, al’umma da dama sun yi ta taya shi murna, suna bayyana farin cikinsu ga cigaban.

Al'umma da dama na ganin karin girma yana da matukar muhimmanci ga ilimin addinin Musulunci a Najeriya.

Kara karanta wannan

An kai hari kan babban layin wuta a Arewa, yankuna sun shiga duhu

Haka zalika, an yi masa addu’o’in fatan alheri tare da rokon Allah ya kara masa basira da albarka a rayuwa.

An ba malaman addini mukami a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta nada kwamitin shura da zai jagoranci al'amuran addini a jihar.

Legit ta wallafa cewa malaman addinin Musulunci daga kungiyoyi da dama ne za su jagoranci kwamitin tare da hadin gwiwar ma'aikatar addini.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng