Izala Ta Shirya Babban Taro a Abuja, Bala Lau Ya Gayyaci Sheikh Jingir

Izala Ta Shirya Babban Taro a Abuja, Bala Lau Ya Gayyaci Sheikh Jingir

  • Shugaban malaman Izala na ƙasa, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, ya sanar da shirin gudanar da taron kasa da kasa a birnin tarayya Abuja
  • Dr. Jalingo ya ce an kai wa shugaban Izala mai hedikwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, takardar gayyata domin halartar taron
  • Sanarwar ta jawo martanin jama'a, yayin da Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce ba taron Qur'anic Convention ba ne za a gudanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Shugaban malaman Izala na ƙasa, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, ya sanar da cewa ƙungiyar za ta gudanar da wani babban taron kasa da kasa a birnin tarayya Abuja.

Dr. Jalingo ya bayyana hakan ne a wani sako da ya fitar, inda ya ce sun kai wa shugaban Izala mai hedikwata a Jos, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, takardar gayyata domin halartar taron.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

Sheikh Sani Yahaya Jingir da Abdullahi Bala Lau
Sheikh Sani Yahaya Jingir a hagu da Abdullahi Bala Lau a dama. Hoto: Jibwis Nigeria|Hamza Muhammad Sani
Source: Facebook

Dr Jalo ya wallafa sakon ne a Facebook a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar Najeriya da rawar da malaman addini za su taka.

An gayyaci Sheikh Jingir

A cikin saƙon nasa, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya karɓi takardar gayyatar cikin mutunci da nuna 'yan'uwantaka.

Ya ce bambancin jagoranci tsakanin ƙungiyoyin da'awa ba yana nufin bambancin akida ko manufar yaɗa Sunnah ba.

Ya rubuta cewa:

"Tabbas bambancin jagoranci na mutane a fagen da'awah sam ba shi yake nuna, ko kuwa yake wajabta bambancin aƙidar mutanen ba, ko bambancin manufarsu ta yaɗa sunnah ba.
"A kan iya samun ƙungiyoyin da'awah da yawa amma kuma aƙidarsu da manufarsu ta yaɗa sunnah ta zamanto abu guda."

Ba Qur'anic Convention ba ne

Bayan sanarwar, fitaccen malamin addini, Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna, ya yi karin haske cewa taron da za a gudanar ba taron Qur'anic Convention ba ne.

Kara karanta wannan

Malami ya bankado 'sirrin' Tinubu game da neman cin zabe ta kowace hanya

Ya bayyana hakan ne bayan wasu sun fara ɗauka cewa taron da aka sanar shi ne Qur'anic Convention da aka soke gudanarwa a baya saboda ce-ce-ku-ce.

Ya rubuta a Facebook cewa:

"Ba Qur'anic Convention Izalah za ta yi a Abuja ba!. ko dai baka san ma'anar ba ko kungiyar ce baka so!"
Dr Ibrahim Jalo Jalingo da Bala Lau
Sheikh Bala Lau da Dr Ibrahim Jalo Jalingo. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Martanin jama'a kan taron

Sanarwar da Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya fitar ta jawo martani daga mabiyan malamai a kafafen sada zumunta.

Umar Doya ya yi kira ga malamai su ci gaba da kyautata mu'amala tsakaninsu, yayin da Adamu Hassan Kumo ya yi fatan kada a mayar da taron wajen yakin neman zaɓen siyasa.

Mukhtar Yusuf Gummi kuwa ya yabawa matakin haɗin kai tsakanin malamai, yana mai addu'ar Allah Ya haɗa kansu kan Sunnah, yayin da wasu da dama suka yi addu'ar Allah Ya ba shugabannin malamai kariya da nasara.

Malamai sun gana da Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya bayyana cewa malaman addinin Musulunci sun saba ganawa da shugaban ƙasa domin faɗa masa gaskiyar halin da al'umma ke ciki.

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

Malamin ya ce kafin ya tafi Jamhuriyar Nijar, an gayyaci malamai 11 domin ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda suka tattauna da shi kan matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa.

Ya ƙara da cewa bayan irin waɗannan ganawa, malamai ba sa ganin dacewar fito wa su bayyana duk abin da suka tattauna da shugaban sai abin da ya zama dole.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng