Abin da Ya Hana Dr. Rijiyar Lemu Halartar Bikin Bada Kyaututtukan Lamban Girma Ya Fito

Abin da Ya Hana Dr. Rijiyar Lemu Halartar Bikin Bada Kyaututtukan Lamban Girma Ya Fito

  • Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi bayanin yadda ya ji da ya samu lambar girman OON
  • Masanin yace bai yi tunanin zai samu lambar ba domin yana yi ne saboda neman yardar Ubangijinsa
  • Malamin ya aika wani na hannun damansa ya karbi lambar a madadinsa domin bai samu jirgin sama ba

Kano - Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi bayani a game da lambar girmamawa da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ba shi kwanan nan.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yace samun wannan lambar yabo ya nuna an yaba aikin da malamai suke yi.

Sani Rijiyar Lemu ya yi mamakin karrama shi da aka yi, yace bai samu zuwa wajen bikin da kansa ba ne saboda takardar ba ta shigo hannunsa da wuri ba.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Mutum 440 Cikin Wadanda Buhari Ya Ba Wa Lambar Yabo Ya Kamata Suna Gidan Yari

Babban malamin yace sai a daren Litinin da kimanin karfe 11:30 ya samu labarin yana cikin wadanda gwamnatin tarayya za ta ba lambar karramawan.

Babu wani jirgin sama da aka samu wanda zai je birnin tarayya Abuja daga garin Kano, har a samu halartar bikin a Aso Villa da karfe 9:00 na safiyar ranar.

Ganin haka, sai shehin ya zabi wani wanda yake Abuja ya karbi lambar girma a madadinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr. Rijiyar Lemu
Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu Hoto: @kabir.asgar
Asali: Facebook

Kwararren masanin hadisin ya fadawa BBC cewa wannan lambar girma da ya samu ya nuna ya kamata gwamnati ta rika kula da aikin da malamai suke yi.

A jawabinsa, malamin yace samun shaidar OON kwarin gwiwa ne ga shi da ire-irensa wadanda suke aiki dare da rana domin rainon zuciyar Bayin Allah.

Sani Rijiyar Lemu yace tun farko yana karantarwar ne domin ya samu yardar Allah.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince a Raba Buhunan Kayan Abinci 240, 000 a Wuraren da Aka Yi Ambaliya

Wanene ya wakilci Malam a Aso Rock Villa?

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Alhaji Muhammad Bello Dalha ne wanda ya wakilci Sheikh Rijiyar Lemu, ya karbi wannan lambar girma a madadinsa.

Muhammad Bello Dalha shi ne shugaban kungiyar Sautul Haq mai aikin yada addinin musulunci, kuma shi ne sakataren cibiyar da’awa ta Imam Bukhari.

Kamar yadda bayani ya nuna a shafin babban malamin, Bello Dalha yana cikin manyan mafi kusanci da Sani Rijiyar Lemu, kuma yana daf da zama surukinsa.

An karrama Malaman Musulunci

Kuna da labari cewa a farkon makon nan, Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya samu lambar OON saboda gudumuwar da yake badawa wajen yada musulunci.

Gwamnatin tarayya ta karrama Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemu, Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Dr. Tajuddeen Adigun da lambar karramawa a shekara nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel