Hormuz: Trump Ya Zargi Iran da Gangancin Karya Yarjejeniyar Sulhu da Amurka

Hormuz: Trump Ya Zargi Iran da Gangancin Karya Yarjejeniyar Sulhu da Amurka

  • Donald Trump ya zargi kasar Iran da kai wa wani jirgin ruwa hari lokacin da ya yi kokarin ya bi ta mashigar Hormuz a makon nan
  • Shugaban Amurka ya zargi kasar Iran da abin da ya kira da shashanci ganin cewa an cin ma yarjejeniyar sulhu kuma an dakatar da yaki
  • Wasu jirage marasa matuka ne suka kai wa jiragen ruwan harin, amma duk da haka ba a samu asarar rai ko dukiya a sanadiyyar hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

America - Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi Iran da abin da ya kira ‘sakarcin karya yarjejeniya’ da aka cin ma bayan tsawon lokaci.

Donald Trump ya yi wannan magana ne a sakamakon hari da aka kai wa wani jirgin ruwa a lokacin da ya yi yunkurin ratsawa ta mashigar nan ta Hormuz.

Trump
Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana nuna wa wani yatsa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Donald Trump ya zargi Iran da harin Hormuz

Rahoton da ya fito daga tashar BBC ya bayyana cewa babu wani rai da aka rasa a sakamakon harin da aka kai wa jirgin a ranar Alhamis 25 ga Yuni 2026.

Kara karanta wannan

Kocin kungiyar kwallon kafa ya sha da kyar kan zargin satar mazakuta

Da yake magana a shafinsa na Truth Social a yammacin Juma’a, Donald Trump ya zargi Iran da amfani da makamai wajen harbin wasu jiragen ruwa.

“Karara, an yi sakarcin karya yarjejeniyarmu.”

Donald Trump ya bayyana wa duniya cewa duk da sun rotsa jirage marasa matuki uku, wani daga cikinsu ya yi nasarar yi wa wani jirgi mai tsada rauni.

“An yi wa jirgin dameji, amma dai ya yi nasarar wucewansa.”

Gwamnatin Iran ba ta tanka Donald Trump ba

Daga lokacin da Trump ya yi wannan magana zuwa yanzu da ake tattaro rahoton nan, ba a ji Gwamnatin Iran ta maida wa Amurka martani ba.

Quartz An dai kai harin ne kwanaki kadan bayan Sojojin IRCG na juyin-juya halin kasar Iran sun yi gargaji cewa za su farmaki masu bi ta Hormuz.

Shafin Quartz ya ce bayanan da aka samu daga Birtaniya sun nuna an kai jirgin hari ne a Kudu maso gabashin kasar Oman a ranar Alhamis da ta gabata.

Trump
Shugaban Amurka Donald Trump da wani jirgi a mashigar Hormuz Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ana so a kawo karshen matsaloli a Hormuz

An ce jirgin yana ta bin shawarwarin UKMTO lokacin da aka auka masa, amma dai majiyar ta ce duka wadanda suke ciki ba su samu ko rauni ba.

Kara karanta wannan

Trump ya kawo tsarin da kayan abincin Amurka zai rika zuwa Iran

Shugaban IMO ya sha alwashin hada kai da Amurka da Iran domin ganin karshen wannan lamari.

A cewar IMO, jirage da dama sun wuce ta mashigar bayan an bude Hormuz sakamakon sasantawar da Amurka ta yi da kasar Iran a watan Yulin 2026.

Sai dai an ji mahukuntan kasar Iran sun dage cewa duk wanda zai bi ta mashigar sai ya biya kudi, zancen da Donald Trump bai yi na’am da shi ba.

Lokacin da Iran ta Hormuz

Ana da labari kasar Iran ta bayyana cewa ta hana jiragen yaki na Amurka da Isra'ila shiga mashigar Hormuz amma kasar ta musanta wannan ikirarin.

Hakan ta faru ne bayan Donald Trump ya sanar da cewa Amurka za ta jagoranci fitar da jirage da suka makale a mashigar, abin da Iran ta ce karya yarjejeniya ne.

Rundunar Amurka ta tabbatar cewa ba wani jirgin nata da aka kai wa hari, tana ci gaba da ayyukanta na toshe hanyoyin jiragen ruwan Iran yayin da ake ta yaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng