Sojoji Sun Gwabza da Lakurawa 300, an Rasa Rayuka bayan Yin Jina Jina

Sojoji Sun Gwabza da Lakurawa 300, an Rasa Rayuka bayan Yin Jina Jina

  • Ana fargabar cewa wasu ‘yan ta’addan Lakurawa sun kashe sojoji hudu yayin da suka kai hari wani gari da ke ƙaramar hukumar Kebbe a jihar Sokoto
  • Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan, sama da 300, sun shiga garin a kan babura, inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro tare da kai hare-hare wurare
  • Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe ranar Juma’a, yayin da sojojin da ke sansanin soja a wajen garin suka buɗe wuta kan maharan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Ana fargabar cewa ‘yan ta’addan Lakurawa sun kashe sojoji hudu yayin wani hari da suka kai Kebbe a jihar Sokoto.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga garin da adadi mai yawa na babura, inda suka yi artabu da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ɗana tarko a cikin dare, sun rutsa wasu mutane da ke hanyar zuwa Abuja

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a jihar Kwara. Hoto: Kwara State Government
Source: Facebook

An yi musayar wuta da sojoji

Punch ta wallafa cewa wani masanin harkokin tsaro a Sokoto, Bashar Altine, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sojoji hudu ake fargabar an kashe yayin musayar wutar.

Sai dai ba a samu tabbacin kai tsaye kan adadin wadanda suka mutu ba a lokacin da aka haɗa rahoton.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, Ahmed Rufai, ya kuma tabbatar da faruwar harin, amma ya ce rundunar na ci gaba da tattara bayanai.

Rufai ya ce ba zai iya tabbatar da ko an samu asarar rayuka ba, ciki har da rahoton mutuwar sojoji hudu.

An farmaki shaguna da asibiti

A cewar Altine, bayan musayar wuta da sojoji, maharan sun shiga cikin garin Kebbe, musamman yankin Sabon Gari.

Ya ce ‘yan ta’addan sun balle wasu shaguna tare da kwashe wayoyin hannu da burodi masu yawa.

Maharani sun kuma buɗe wuta kan wata motar soja da ke ɗauke da makamin roka, inda suka lalata tayoyin uku tare da farfasa gilashin motar.

Kara karanta wannan

Miyagu daga kabilar Tibi sun hallaka direban Dangote da wata mata a Benue

Taswirar jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An kai hari babban asibitin Kebbe

Altine ya ce daga bisani maharan sun nufi Babban Asibitin Kebbe, inda suka farfasa gilashin wasu motocin da aka ajiye a harabar asibitin.

Ya ce motocin da aka lalata sun haɗa da motar Jami’in ‘Yan Sanda na wajen wato DPO, da kuma motar ɗaukar marasa lafiya.

“Sun kuma kwace wayoyin hannu na wasu marasa lafiya da ke asibitin,”

In ji shi.

Sahara reporters ta wallafa cewa maharan sun kwashe babura hudu na wasu mazauna garin yayin da suke shirin ficewa daga Kebbe.

A cewar masanin tsaron, maharan sun bar garin Kebbe da yamma ta hanyar wajen ofishin ‘yan sanda. Ya ce daga nan suka nufi wasu al’ummomi da ke yammacin garin.

An cafke masu garkuwa a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta cafke mutane shida da ake zargi masu garkuwa da mutane ne tare da lalata maboyarsu a kauyen Dogon Pako da ke ƙaramar hukumar Ikara.

Kara karanta wannan

Hukumar alhazai ta sanar da kuɗin kujerar hajjin shekarar 2027 a jihar Kano

An cafke waɗanda ake zargin ne ranar Talata bayan wani wanda ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane ya bai wa ‘yan sanda bayanai.

Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce wanda aka yi garkuwa da shi ya bai wa ‘yan sanda cikakken bayanin gidan wani mai suna Ja’e Samalu, mai shekaru 65, inda aka ce an tsare shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng