Bayan Abin da Ya Faru Ranar Juma'a, Amurka Ta Kawo Sabon Hari Najeriya

Bayan Abin da Ya Faru Ranar Juma'a, Amurka Ta Kawo Sabon Hari Najeriya

  • Dakarun sojin Amurka da na Najeriya sun sake kai farmaki kan mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP a Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Rundunar sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afirka (AFRICOM) da hedkwatar tsaron Najeriya sun tabbatar da kai hare-haren yau Litinin
  • Hedkwatar tsaro ta kuma sake jaddada kudurinta na kare ikon Najeriya da tsaron kasar, tana mai cewa za ta ci gaba da daukar matakin murkushe ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rundunar sojin Amurka mai kula da Afirka (AFRICOM) tare da dakarun Najeriya sun sake yin luguden wuta kan mayakan kungiyar ISWAP a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Harin ya biyo bayan kashe wani babban kwamandan ISIS mai suna Abu-Bilal al-Minuki (Abu Mainok) tare da wasu daga cikin mayakansa a ranar Juma’a da ta gabata.

Kara karanta wannan

APC ta hana 'yan siyasa 47 shiga takarar sanata, ta saki cikakken jerin sunayen

Shugabanni.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

A wata sanarwa da AFRICOM ta wallafa a shafinta na X yau Litinin, ta ce babu wani sojan Amurka ko na Najeriya da ya samu rauni yayin kai harin.

An kashe mayakan ISWAP 20 a Najeriya

Da take magana kan farmakin, Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta ce an kashe fiye da mayakan ISIS/ISWAP 20 a harin.

Daraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa an kai harin ne kan maboyar ‘yan ta’adda a yankin Metele da ke Arewacin jihar Borno, wuri da ya zama matattarar yan ta da kayar baya.

A cikin sanarwar, ya ce an gudanar da harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna motsi da taruwar ‘yan ta’adda a yankin.

Najeriya ta tashi tsaye kan matsalar tsaro

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa sabon farmakin wani bangare ne na ci gaba da gudanar da hare-haren yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas domin rusa hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda da hana su samun mafaka a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano

“Wadannan hare-hare sun biyo bayan kashe kwamandan ISIS, Abu-Bilal al-Minuki, kuma wani bangare ne a kokarij tarwatsa hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda, kawar da su da hana su samun mafaka a cikin Najeriya,” in ji sanarwar.
Sojojin Najeriya.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojojin Najeriya sun shirya kare Najeriya

Rundunar sojin ta kuma sake jaddada kudurinta na kare ikon Najeriya da tsaron kasar, tana mai cewa za ta ci gaba da daukar matakin murkushe masu tada kayar baya.

Manjo Janar Uba ya kara da cewa:

“Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da kare iko, tsaro da cikakken yancin kasar nan. Duk wani dan ta’adda da ke barazana ga jama’a, al’umma da zaman lafiyar kasa za a gano shi kuma a murkushe shi.
"Ba za a bari ‘yan ta’adda su samu mafaka a ko’ina cikin Najeriya ba."

Yadda sojoji suka kashe kwamandan ISIS

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Amurka da na Najeriya sun fafata da 'yan ta'addan kungiyar ISIS a yankin Tafkin Chadi yayin da suka farmaki sansanin Abu Mainok.

Sojojin sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan ISIS na tsawon fiye da sa’o’i uku kafin su yi nasarar kashe Abu-Bilal Al-Minuki, wanda aka fi sani da Abu Mainok.

Jami’an sun bayyana cewa da farko sojojin Amurka sun yi ƙoƙarin kama Al-Minuki ne da rai, amma sai suka kashe shi ta hanyar harin jirgin sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262